Friday, 12 July 2019
Za a sayar da wasikar da Tupac ya rubutawa Madonna domin su rabu akan kudi naira miliyan 108

Home Za a sayar da wasikar da Tupac ya rubutawa Madonna domin su rabu akan kudi naira miliyan 108
Ku Tura A Social Media
Kotun koli ta birnin New York ta bayar da umarnin sayar da wasikar da shahararren mawakin nan na kasar Amurka Tupac ya aikawa Madonna

- A cikin wasikar Tupac ya bukaci cewar yana so alakarsa da Madonna ta zo karshe, saboda irin yadda yake samun barazana ta launin fata

- A yanzu dai wani kamfani yayi hasashen cewa wasikar kudin ta zai kai kimanin naira miliyan dari

Kotun koli ta birnin New York ta bada umarnin a sayar da wasikar da shahararren mawakin nan na kasar Amurka Tupac Shakur ya rubutawa budurwarsa Madonna lokacin yana gidan yari akan cewar yana so su rabu.

Kotun ta bayyana cewa wasikar yanzu ta zama mallakin wani kamfani mai suna "Gotta Have Rock and Roll", duk da dai wasu kungiyoyi sun bukaci cewa kada a sayar da wasikar.

Kamfanin ya samu wasikar daga gurin wani tsohon na hannun daman Madonna mai suna Darlene Luts, kuma sun gama shiri tsaf domin sayar da ita ga wanda ya biya farashi mai yawa a ranar 17 ga wannan wata na Yuli.


Tupac ya rubuta wasikar da hannunsa mai shafi uku, a lokacin da yake gidan yari a shekarar 1995, daidai lokacin da yake da shekaru 24 a duniya. A cikin wasikar ya kawo karshen alakarsa da Madonna, wacce take da shekaru 37 a lokacin. Rubuta wasikar da shekara daya Tupac ya mutu.

"Dole na baki hakuri," ya rubuta. "Kamar yadda kika ce ni ba abokine na kwarai ba. Ba kuma hakan yana nufin ni azzalumi bane, ko kuma saboda baki cancanci na soki ba, aa matsalar wariyar launin fata yasa ya zama da wahala bakin mutum irina ya dinga soyayya da baturiya kamar ki."

Wani kamfani mai suna Memorabilia yayi hasashen cewa za a iya sayar da wasikar akan kimanin kudi naira miliyan 108.

Yanzu haka dai an sanyawa wasikar karancin kudin da za a sayar da ita shine naira miliyan 35.

@legit

Share this


Author: verified_user

0 Comments: