Wednesday, 31 July 2019
Yan wasan kwallon kafa 10 masu takarar gwarzon FIFA na bana

Home Yan wasan kwallon kafa 10 masu takarar gwarzon FIFA na bana
Ku Tura A Social Media
Hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA, a ranar Laraba ta bayyana jerin sunayen 'yan wasan kwallon kafa guda goma masu takarar gwarzon shekarar 2019.

Hukumar FIFA ta ce a halin yanzu kofar fara jefa kuri'u a bude take domin tantance gwarzon bana. 'Yan wasa, masu horaswa wato koci, masoya da kuma 'yan jaridu na kwallon kafa su ne za su tantance gwarzon bana.

Ga dai jerin 'yan wasan kwallon kafa goma tare da kasashensu da za su fafata wajen takarar gwarzon bana kamar yadda hukumar FIFA ta bayyana:

1. Lionel Messi - Argentina

2. Sadio Mane - Senegal

3. Muhammad Salah - Egypt

4. Cristiano Ronaldo - Portugal

5. Harry Kane - England

6. Matthijs de Ligt - Netherlands

7. Frenkie de Jong - Netherlands

8. Virgil van Dijk - Netherlands

9. Kylian Mbappe - France

10. Eden Hazard - Belgium

Hukumar FIFA ta kuma fidda masu takarar kocin da yafi taka rawar gani a bana kamar haka:

1. Mauricio Pochettino - Tottenham

2. Djamel Belmadi - Algeria

3. Didier Deschamps - France

4. Marcelo Gallardo - River Plate

5. Erik Ten Hag - Ajax

6. Tite - Brazil

7. Fernando Santos - Portugal

8. Pep Guardiola - Manchester City

9. Jurgen Klopp - Liverpool

10. Ricardo Gareca - Peru

Share this


Author: verified_user

0 Comments: