Wednesday, 24 July 2019
Ya kamata a Sanya doka kan was’azi a Najeriya inji Jaafar Jaafar

Home Ya kamata a Sanya doka kan was’azi a Najeriya inji Jaafar Jaafar
Ku Tura A Social Media


Mawallafi jaridar Daily Nigerian wanda yayi kaurin suna wajen fallasa bidiyoyin dollar na gwamna Ganduje  yayi rubutu kan rikicin shi’a da ya tashi a Najeriya.

Jarumin ya dakko dogon tarihi inda ya hado tun daga maitatsine har zuwa yadda shi Zakzakin ya fara da’awa a ABU zaria.

Cikin rubutun Jarumin yayi misali na yadda kin daukar shawarar masana aikin tsaro musamman na SSS ya janyon iftilai kala kala tun daga maitastine har zuwa Boko Haram.

Jarumin dan jaridar yace " Akwai bukatar a dauki matakin kawo doka wadda zata kula da wa’azi musamman a yankin Arewacin Najeriya. 

Yace hakan ne kawai zai iya kawo karshen yadda wasu malamai ke shiga rigar addini amma su rinka siyasa

Duk da cewa gwamnatin Kaduna ce ke neman kawo dokar a yunzu haka, yunkurin kawo dokar yiwa malamai rijista ta samo asali ne a wani zango daga gwamnatin Dr Rabiu Musa Kwankwaso ta Kano wadda ta kawo tsare-tsare dayawa da ake aiki da su a fadin Najeriya a yunzu irinsu TSA da dai sauransu.

Cikin yunkurin dokar ta kwankwaso, za’a dawoda majalisa wadda ke da iko kamar majalisun sarakunan gargajiya wadda kuma zasu binciki akidun duk wani malami da yake son yayi wa’azi kafin a bashi ikon yin hakan.

Tabbas, harkar addini ta gurbace a Najeriya inda malamai suka shiga siyasa wasuma har sukan abokan gaba sukeyi domin ayi musu nadin ministoci ko kwamishinoni" Inji Jaafar Jaafar

Share this


Author: verified_user

0 Comments: