Thursday, 25 July 2019
Wata sabuwa: An kusa daina sanya Zee Preety a harkokin fina-finan Hausa - Adam A Zango

Home Wata sabuwa: An kusa daina sanya Zee Preety a harkokin fina-finan Hausa - Adam A Zango
Ku Tura A Social Media
A wata hira da aka nuno fitattun jaruman Kannywood guda biyu Adam Zango da Zpreety,an nuno su suna daukar wani bidiyo tare

- An dai jiyo muryar jarumin yana bayyanawa jarumar cewa an kusa daina sanya ta a shirin fim din Hausa

- Inda ita kuma ta nuna ba damuwarta bane tunda dai har za ta dinga yin bidiyonta a kananan wayoyi tana turawa duniya suna gani

A wani bidiyo da aka hasko fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood Zulaihat Ibrahim wacce aka fi sani da Zpreety, an hasko ta tana cin abinci, yayin da shi kuma shahararren jarumin nan Adam A Zango yake daukarta a bidiyo.

A hirar da suka yi a cikin bidiyon an jiyo muryar jarumin Adam Zango yana yiwa jarumar magana akan cewa an kusa a daina sanya ta a cikin fina-finan Hausa na Kannywood.


Ga dai yadda hirar ta su ta kaya:

Zango: Zee kin san cewa wallahi an kusa daina saka ki a fim din Kannywood gaba daya.

Zee: Wai da gaske kake?

Zango: Kwarai kuwa!

Zee: To dan Allah idan suka bar saka ni kai zaka sani?

Zango: Sosai ma kuwa zan dinga saka ki.

Zee: Zaka cigaba da bani irin wannan abincin, da kuma irin wannan kwalliyar da ake yi mini?

Zango: Kwarai kuwa harda motar nan da kika ce taki ce zan baki.

Zee: To kada su saka din, kada Allah yasa su saka ni, dama ni ban damu da wannan fim din ba, nafi so na dinga yi a kananan wayoyi.

A cikin bidiyon fitacciyar jarumar ta nuna cewa suna kasar Habasha ne, kuma daga nan zasu wuce kasar Kenya, inda ta kara da cewa Adam Zango wanda take kira da Baba Ado bai gajiya da wahala da su.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: