Saturday, 6 July 2019
Wasu Dabarun Raba Budurwa Da Saurayinta

Home Wasu Dabarun Raba Budurwa Da Saurayinta
Ku Tura A Social Media

Da akwai wasu matan da yanzu haka suna cikin soyayyar da basu samun kulawa wajen samarin nasu kamar yadda ya kamata. Duk kuwa da akwai soyayya a ransu ga wadannan samarin. Wasu kuwa suna soyayya ne da samarin da basa kusa dasu, m'ana basa gari daya, jiha daya ko kasa daya. Idan har ka kyala ido kaga wata cikin irin wannan yanayin kuma kana sonta, to ga wasu dabarun da zaka rabata da wancan.

Kayi kokarin samun kusanci da ita wannan shine zai baka damar aiwatar da kudirinka cikin sauki.

Nuna mata kulawa ta hanyar sakonnin text da yawan kiranta a waya zai karkatan da zuciyarta gareka. Mata suna son kulawa.

Ka binciko abunda take sonci ko sakawa ka mata kyautansu.  Mata suna son kyauta.
Idan kasan ranar haihuwarta yi mata kyauta na bajinta  wannan ma na iya sace zuciyarta.
Hiranka da ita ya kasance kana mata zancen abubuwan datakeson jine ba masu bata mata rai ba.

Ka rika kusantar 'yan uwanta kana yiwa kannenta kyaututtukan jawo hankali.
 Allah bada sa'a

Share this


Author: verified_user

0 Comments: