Thursday, 11 July 2019
To fah: Ina son Sa'eed wanda matarsa ta cakawa wuka - Inji Ummi Abdullahi Kaduna

Home To fah: Ina son Sa'eed wanda matarsa ta cakawa wuka - Inji Ummi Abdullahi Kaduna
Ku Tura A Social Media
Wata kyakkyawar budurwa dake zaune a jihar Kaduna ta nuna soyayyarta ga Sa'eed wanda matarsa ta caka masa wuka a kirji

- Ta bayyana cewa tana mutukar sonsa, saboda tun lokacin da ta samu labarin abinda ya faru dashi taji ya kwanta mata a zuciya

- Ummi ta bayyana cewa ita bata taba yin wani abu Facebook ba, amma saboda soyayyar da take yiwa Sa'eed yasa dole ta bude shafin

Wata budurwa mai suna Ummi Abduollahi dake zaune a cikin birnin Kaduna ta nuna soyayyarta ga mutumin nan dan jihar Kano da matarsa ta cakawa wuka a kahon zuci.

Ummi ta bayyana cewa tun lokacin da ta samu labarin abinda ya faru da Sa'eed kawai taji soyayya da tausayinsa ya kamata, saboda haka ita tana yi masa soyayya ce irin ta aure.


Ga abinda Ummi ta rubuto:

"Dan Allah ku isar mun da sakona cewa ina son Sa'eed da aure, saboda tun ranar da matarsa ta caka masa wuka naji ina sonsa da aure, kuma ina kaunarsa matuka, hasali ma saboda shi na bude shafin Facebook.

"Na tausaya masa kwarai da gaske, kuma ina yi masa addu'ar Allah ya bashi lafiya."

Sa'eed dai shine mutumin da matarsa ta cakawa wuka a kahon zuci makonnin da suka gabata, inda ake zargin cewa bashi da aiki sai dukan matar tasa, sai dai kuma bayan ya farfado labarin ya canja, domin kuwa ya fede biri har wutsiya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: