Tuesday, 2 July 2019
Tirkashi: Na sha kama mijina dumu-dumu yana zina da mata akan gadonmu na Sunnah

Home Tirkashi: Na sha kama mijina dumu-dumu yana zina da mata akan gadonmu na Sunnah
Ku Tura A Social Media


- Wasu ma'aurata da suka kai kara kotu, sun nemi kotu ta raba auren dake tsakaninsu saboda cin amanar juna da suke

- Matar ta bayyanawa kotun cewa ta sha kama mijin nata yana lalata da mata akan gadonsu na sunna a lokuta da dama

- Haka shi kuma mijin ya bayyana cewa matar tana yawan yi masa barazanar cewa zata yi masa wanka da ruwan guba idan har bai daina abinda yake ba

Rikici tsakanin wasu ma'aurata, kan cin amanar juna yasa sun nufi kotu da niyyar ta raba auren dake tsakanin su.

Wata mata mai suna Misis Edith Obieme ta bukaci wata kotu dake birnin Legas akan ta raba auren dake tsakaninta da mijinta mai suna Mista Kingsley, wanda suka shafe shekara biyu suna tare, matar ta bayyanawa kotu cewa ta sha kamashi yana lalata da mata a lokuta da dama a kan gadonsu na Sunnah.

Da farko dai mijin shine wanda ya fara kai karar kotun, inda ya nemi kotun ta raba auren nasu, akan cewar matar tasa tana yawan yi masa barazanar za ta halaka shi, sai dai ita kuma matar ta musanta zargin da mijin yayi mata.

Matar ta bukaci kotun ta raba auren nasu saboda ta gaji da ganin yadda mijin nata yake kwanciya da mata akan idonta ba tare da ya damu ba.

"Na taba kama shi da 'yar aikin gidanmu, tunda nake dashi ban taba ce mishi ina bukatar 'yar aiki ba, amma tun daga ranar dana kamasu ta kwashe kayanta ta bar gidan.

"Mijina talaka ne bashi da ko sisi, ina ganin babu wata riba da zan ci idan na kashe shi," in ji kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).

"Na san dai na taba yiwa karuwarsa barazanar cewa zanyi mata wanka da ruwan guba (ACID) idan na sake ganinta tare dashi," in ji Edith wacce take kasuwancin ta kuma tana goyon yaro dan watanni hudu.

Ta kuma bayyanawa kotu cewa ita ce take daukar duka nauyin gidan, tun daga kansa, 'ya'yansa da kuma matansa da ya saka.

Sai dai kuma mijin ya bayyama cewa duk lokacin da suka yi fada da ita sai tayi mishi barazanar cewa zata yi masa wanka da ruwan guba.

"Ba na son na mutu, ni kuma gaskiya ina tsoron wata rana za ta kasheni."

"Ba na son na mutu, ni kuma gaskiya ina tsoron wata rana za ta kasheni."

"Na jima bana cin abincinta, saboda ina tsoron kada ta sanya mini guba," in ji mijin.

Ma'auratan dai sun nemi kotu ta raba auren nasu, inda kotun ta daga sauraron karar har zuwa ranar 18 ga watan Yuli, bayan ta gama sauraron kowanne bangare a tsakaninsu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: