Thursday, 25 July 2019
Tirkashi: Baza ka taba burge Hausawa mu ba sai ka sanya hotonka rungume da karuwa a daki - Jarumi Alin Shaba

Home Tirkashi: Baza ka taba burge Hausawa mu ba sai ka sanya hotonka rungume da karuwa a daki - Jarumi Alin Shaba
Ku Tura A Social Media
A wani bidiyo da yake yawo a shafukan sada zumunta an hasko jarumi Alin Shaba yana zagin mutanen da suka zage shi saboda yayi bidiyo rungume da matarsa

- Shaba ya bayyana cewa 'yan wasa da yawa sun dauki hotuna da bidiyo rungume da matan da ba nasu ba, amma babu wanda ya taba yin magana sai shi da yake nuna soyayya ga matarsa

- Ya ce ya san yawancin masu zagin shi 'yan luwadi ne masu neman maza 'yan uwansu

Idan ba a manta ba a kwanakin baya an gano bidiyon jarumin nan dan wasan Hausa Alin Shaba rungume da matarsa, inda bidiyon ya dinga yawo a shafukan sada zumunta, kuma mutane da yawa suka dinga Allah wadai da wannan bidiyon.

A wannan karon jarumin ya fito ya caccaki mutanen da suka dinga zagin shi, inda ya bayyana cewa shi bai san yadda aka yi wannan bidiyo ya hau shafin Youtube ba domin kuwa shi dai ya san a iya shafin Instagram din shi ya sanya.

A hirar an jiyo muryar wani mutumi yana yiwa jarumin tayin abinci, sai dai kuma shi jarumin ya nuna cewa ba zai iya cin komai ba saboda yana tunanin matarsa.


Ga abinda jarumin ya ce:

"Kasan Hausawan mu ba zaka taba burgesu ba idan ba da karuwa kayi bidiyo ba, idan kana so ka burge Hausawan mu to kayi bidiyo da karuwa ko ka rungumeta kayi hoto, to a nan ne zasu fara yabonka.

"Amma ya za ayi Allah ya bamu mata suna son mu muna son su amma kuma baza mu nuna musu soyayya ba, sai dai mu dinga fitowa muna nunawa karuwai na titi soyayya, haka mutunci ne?

"Sannan dan nayi bidiyo da matata laifi ne? Da har za a dinga zagi na, Sani Danja ya rungumi mace yayi bidiyo da ita, Rahama Sadau tayi bidiyo an rugume ta, jaruma Empire ita ma tayi bidiyo ita da mijinta.

"Sai kawai ni dan nayi da matata cikin mutunci, sai a dinga zagi na.

"Na san yawancin mutanen da suke zagi na 'yan luwadi ne, saboda idan ba 'yan luwadi ba babu yadda za ayi ka dauki hoto da matarka a dinga zaginka.

"Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi, idan yazo wajen iyalinsa sai ya rungumesu ya sumbace su, balle mu kuma da bamu kai shi daraja ba."

Share this


Author: verified_user

0 Comments: