Thursday, 4 July 2019
Tasirin Da Fa'idojin Auren Bazawara Ko Wacce Ta Girmeka A Shekaru

Home Tasirin Da Fa'idojin Auren Bazawara Ko Wacce Ta Girmeka A Shekaru
Ku Tura A Social Media


Daga Anty Hauwa Kaduna

Yana daga wasu fa'idoji da namiji zai samu in ya auri matar data girmeshi ko bazawara kamar haka.

☛ nafarko zai sami ladan sunna biyu wato sunnar aure data kuma koyi da annabin rahama s.a.w ya auri wacce ta girmeshe. ,musamman ma inya yiyi dan koyi da fiyayyen halitta s.a.w.

☛ auren mace wacce tafika shekaru akwai yuyuwar samu ingantacciyar ra'yuwar aure matuqar akwai soyayya sakamakon cewa ita ta zauna dawasu mazan tasan rayuwar aure,tasan mai namiji yakeso tasan maye baya so tasami kwarancewar iya kwanciya da miji sabo dahaka da zarar ka auri irin wan nan kuma akwai so daqauna da tarbiyya to ba ma auren dayafi shi dadi,sakamakon tasami working expereence koda bata taba aureba a baya shekarun data yi a rayuwarta zaisa taga abubuwa kalakala a rayuwarta wadanda zasu zame mata darasi a zamantakewar aure nan gaba.

Haqiqa bazawara tafi budrwa sanin makamar aiki a zamantakewar aure musamman ma in tasami saurayi wato wanda tagirma musamman ma ace akwai soyayya.

☛ bazawara tana da haqurin zaman takewa fiye da budurwa dan ita tasan yauda kullum a aikace bawai abaka ba dan tagani akan wasu tagani akan kanta,sabanin budurwa ita kawai tagani akan wasune kawai.

☛ bazawara ko wacce tafika shekaru tarigaya tasan halayen iyayan miji da yadda ake zama da su sabanin budurwa.

☛ ayyukan gida da kula dagida gyaran daki ,iya girki da tsaftace shi , kula da yara da shauran su dukkan su zawarawa sunfi yanmata qwarewa a kai.

☛ dadadan kalamai da kisisina da iya rarrashin miji ,rashin katobara yayin zance.dadin shira dukka zawarawa sun kwarance fiye da yan mata.

*rashin alma bazzaranci da dukiyar maigida .kamar bata abunci wasa dashi da sauransu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: