Thursday, 4 July 2019
Tafa Ta Ƙare : Saudiyya ta gayyaci Nikci Minaj ta bude musu taron waka da Bismillah

Home Tafa Ta Ƙare : Saudiyya ta gayyaci Nikci Minaj ta bude musu taron waka da Bismillah
Ku Tura A Social Media


Kasar Saudiyya ta gayyaci shahararriyar mawakiyar kasar Amurka Nikci Minaj, domin ta yi musu waka

 - Kasar ta gayyace ta ne domin gabatar da wakar a wani biki da zata gabatar ranar 18 ga watan Yuli

- Hakan ya biyo bayan kokarin da kasar take yi na ganin ta kawo cigaba ta fannin sassauta wasu dokoki da ta sanya a shekarun da suka gabata Kasar Saudiyya ta gayyaci shahararriyar mawakiyar nan ta kasar Amurka, Nicki Minaj, domin ta yi musu waka a kasar a cikin wannan watan da muka shiga.

 Kasar ta gayyaci Nicki Minaj ne domin bude musu taron wakar da Bismillah, a yayin da suke shirin gabatar da wani biki a ranar 18 ga watan Yuli, bayan ita kuma kasar ta gayyaci, DJ Steve Aoki da kuma Liam Payne.


 Bayan haka kuma kasar ta bude shafin da mutane masu son ziyara kasar wani shafi da zasu samu bisa cikin sauki. Kasar ta Saudiyya a kwanan nan ta bayyana yadda take so ta daina amfani da wasu dokoki da take amfani da su shekaru da dama.

 Shekaru 35 da suka wuce, kasar ta cire dokar zuwa gidan kallo, sannan kuma kasar ta bai wa mata damar yin tuki a wannan karon. Wannan shekarar, Mariah Carey tayi waka a kasar ta Saudiyya, kasar ta bayyana cewa hakan yana daya daga cikin yunkurin da take na ganin ta kawo cigaba. Sannan tana yin hakan ne domin jawo hankalin mutane su dinga kai ziyara kasar.

@legit

Share this


Author: verified_user

0 Comments: