Friday, 12 July 2019
Ta kone mijinta saboda zai karo mata kishiya a jihar Kano (Hotuna)

Home Ta kone mijinta saboda zai karo mata kishiya a jihar Kano (Hotuna)
Ku Tura A Social Media

Daga Anas Saminu Ja'en

Lamarin ya faru ne a nan jihar Kano kamar yadda na bibiyi ainihin abun an shaida min cewar Mallam Aliyu Ibrahim Fayan-fayan malamin  makarantar firamare ne a Dambatta, inda a daran jiya yana kwance matarsa ta tafasa ruwan zafi kuma ta kwara masa ruwan zafi gaban sa kamar inda kuke gani, kamar yadda na zanta da abokina dan jarida Amb Auwalu Nakarkata Dambatta.

Kuma Mallam Aliyu Ibrahim ya ce shi dai ya san ya fadawa Matarsa cewar zai shi zai kara aure, har ma ya bata kudade domin taje tayi siyayya irin kayan fadar kishiya to tun lokacin da ya fada mata ba su sami matsala da ita ba har take gayamasa cewar su zasu je su hado kayan ma, ko jiya da ya fito zai shiga cikin garin Dambatta sai da ta bashi sautun siyayya ya yi mata ina kwance bayan Nagama jin taskar labarai to har na fita na siyo musu nama suka ci dama na tarar da ita tana dafa ruwan zafi naje na kwanta Kawai sai naji ta kwara min ruwan zafi kamar yadda kuka ganin shi, Inji mijin.

Ya kara da cewar dan kurum nace zanyi karayin aure ne shiya sa 'yan uwana duk sun san zanyi aure, amma har yanzu ban san inda take domin lokacin da abin ya faru wani mafwabci na ne ya  taimakeni ya kawoni nan Asibitin inda nake kwance.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: