Friday, 26 July 2019
Shaharar Mawaki DJ Abba A 2019

Home Shaharar Mawaki DJ Abba A 2019
Ku Tura A Social Media
Tun bayan da mawakin Haruna Abdullahi wanda aka fi sani da Dj Abba ya saki Bidiyon wakar sa mai taken Rawa wanda suka yi tare da fitaccen mawakin Legas mai suna Young6id, tauraruwar sa take kara ci kamar wutar murhu, har kawo yau kullum kara samun magoya baya yakea shafukan sa na kafar yada labarai na zamani, musamman Instagram.
A cikin kwanan nan ya samu kwantiragi da Kungiyar Mr. Eazi wacce aka fi sani da emPawa Africa, inda suka samu damar yi mai bidiyon waka guda daya mai taken ‘Kumatu’.
Duk da cewa mawakin ya nuna rashin jin dadin sa, gani yadda shi kadai ne a Arewa ya samu damar shiga kungiyar ta ‘emPawa Africa’.
Wakar ‘Kumatu’ dai ta samu karbuwa sosai a duniya musamman a Afrika, wacce ake gani bai taba wakar da ta samu mutanen da suka bibiye ta a You tube kamar wakar ba, don akalla mutum dubu 86 suka kalli bidiyon wakar, in da a yanzu haka, a yadda hasashe ya nuna, mawakin DJ Abba yafi ko wani mawakin Hausa Hip hop tarin magoya baya a kafafen yada labarai.
San nan daga baya kuma ya sake sakar wani bidiyon wakar sa mai suna ‘YNS Cypher 2019’ wanda suka yi tare da ‘yan uwansa kamar su Jigsaw, Teswag, da Lil prince, wakar itama ta samu karbuwa sosai, ganin yadda suka tsaya suka tsara ta, musamman yadda labarin ya zama bakon abu a gun mawaka baki daya, itama wakar ‘YNS Cypher2019’ akalla mutane dubu 78 suka kalla a You tube.

Mawaki Dj Abba dai dan asalin garin Kaduna ne, wanda a yanzu haka yana karatu a ABU zaria inda yake aji hudu, yana karantar KS, ya tabbatar mana da hakan ne a wata zantawar da suka yi da wakilinmu kwanan bayan nan.
In da ya kara da cewa yana godiya ga Allah kwarai, da yake kara haskaka masa tauraron sa, in da yake cewa yana so ya ta kara tafiya har sai inda Allah yayi da shi.Ya kuma ce lallai duk lamarin da suke faru da shi cikin kwanan nan, bai taba tsammani ba, dika yin Ubangiji ne, mutum bai isa ya tsara ma kansa ba.

A karshe kuma yace, “ina kara gode ma mutanen da suka bani goyon baya tin daga tushe, kama lokacin da na fara waka kawo yanzu, ina kara gode ma magoya bayana, kuma insha Allahu bazan baku kunya ba zan ci gaba da kawo maku sabbin abubuwa.”

Share this


Author: verified_user

0 Comments: