Wednesday, 3 July 2019
Rashin miji ne ya hanani yin aure –Maryam Yahaya

Home Rashin miji ne ya hanani yin aure –Maryam Yahaya
Ku Tura A Social Media


A wata hira da Freedom Radio tayi da jaruma Maryam Yahaya ta bayyana dalilin da ya hanata yin aure inda tace “da aure da mutuwa duk lokacine, idan lokacina yayi ai zan daga, babu mijinne, ku fito ku aureni, rashin miji ne ya hanani yin aure, kun san maza na wuya yanzu”

Jaruma Maryam Yahaya ta kara da cewa ta cimma nasarori da dama a sana’arta ta film wanda ba zasu kirgu ba, kuma babu abinda zata cewa masana’antar fina-finan hausa sai godiya, a bangaren kalubale kuwa Maryam tace babban kalubalen da ta fuskanta shine da farko iyayenta basu amince ta shiga film din ba, a lokacin da ita kuma tana matukar son ganin ta shiga, sai dai a karshe fitaccen jaruminnan Ali Nuhu yaje wurin mahaifinta ya tambayeshi sannan ya barta ta fara film

Shin ko yaya kuke kallon wannan batu?

Share this


Author: verified_user

0 Comments: