Labarai

Next Level : Tsofafin Ministoci 12 Da Zasu Koma cikin Sabuwar Gwamnatin Buhari

Lai Mohammed, Fashola, Hadi Sirika, Amaechi, Zainab Shamsuna, Darlung, Onu Na Daga Cikin Tsoffin Ministoci 15 Da Buhari Zai Sake Ba Su Mukamin Minista

Kachikwu, Aregbesola, Adebayo, Ambode su ma sun shiga sahu

Daga Aliyu Ahmad

Rahotanni daga majiya mai tushe sun tabbatar da cewa 12 zuwa 15 daga cikin tsoffin mininstoci za su sake samun mukamin minista a zango na biyu na mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

Bincike ya nuna cewa sunayen tsoffin na cikin takarda mai dauke da sunayen sabbin ministocin da aka aikawa shugaban majalisar Dattijai, Sanata Ahmed Lawan a jiya Laraba.

An ce Shugaba Buhari na shirin sake baiwa wasu daga cikin tsoffin ministocin mukamai ne bisa cancantarsu.

Tsoffin ministocin da rahotanni suka nuna suna daga cikin sunayen sabbin ministocin sun hada da tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami ( SAN); Adamu Adamu ( ilmi); Hadi Sirika ( jiragen sama); Zainab Ahmed (kudi); Aisha Abubakar (harkokin mata); Lai Mohammed ( yada labarai); Babatunde Fashola (ayyuka, gidaje da wutar lantaki); Rotimi Amaechi (sufuri); Mohammed Musa Bello ( FCT); Suleiman Adamu Kazaure (albarkatun ruwa); Dr. Ogbonnaya Onu (kimiyya da fasaha); Solomon Dalung (matasa da wasanni) da sauransu.

Duk da cewa rahotanni suna nuni da cewa, Dr. Ibe Kachikwu, tsoffin gwamnonin irin su Rauf Aregbesola (Osun), Niyi Adebayo (Ekiti) da Akinwumi Ambode (Lagos) suna daga cikin wadanda aka mika sunayen su, amma majiyar mu ba ta tabbatar da hakan ba.

Majiyar ta tabbatar da cewa wasu tsoffin ministoci irin su Adebayo Shittu (sadarwa) da Okechukwu Enelamah (kasuwanci) ba za su samu dawowa ba.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button