Sunday, 7 July 2019
Najeriya kasa daya ce mai fuska biyu, yayinda Kudu ke cigaba, Arewa na cibaya - El-Rufai

Home Najeriya kasa daya ce mai fuska biyu, yayinda Kudu ke cigaba, Arewa na cibaya - El-Rufai
Ku Tura A Social Media

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a ranar Asabar ya bayyana Najeriya a matsayin kasa wadda ke da fuskoki guda biyu, inda ya ce akwai bangaren Kudanci wanda ke cigaba da kuma bangaren Arewaci wanda ke fama da jahilci, talauci da kuma rashin cigaba.

A cikin jawabin gwamnan ya yi kokarin kamanta Arewacin Najeriya da kasar Afghanistan wadda yaqi ya dai-daita.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a wani taro na musamman da kungiyar Northen Hibiscus ta shirya domin ‘yan Arewacin Najeriya.

Gwamnan ya fadi cewa, domin magance matsalar da yankin Arewa ke fama da shi ya zama wajibi sai gwamnonin jihohin arewa 19 sun hada hannu wuri daya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: