Tuesday, 9 July 2019
Na kama Matata Tana Turawa Saurayinta Hotunta Na Tsiraici (Nude photos) - Mijin Da Matarsa Ta Soke Shi Da Wuka

Home Na kama Matata Tana Turawa Saurayinta Hotunta Na Tsiraici (Nude photos) - Mijin Da Matarsa Ta Soke Shi Da Wuka
Ku Tura A Social Media
Sa’id Hussain, mijin da matarsa, Fatima Musa mia shekaru 21 da haihuwa ta dabawa wuka a Kano ya bayyana nasa bangaren na hakikanin abinda ya gudana a daren da matarsa ta soke shi da wuka tare da bayyana abubuwan da suka haifar da lamarin.
Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 1:30 na daren ranar Asabar 22 ga watan Yunin, 2019 a gidan ma’auratan da ke a unguwar Mai Kalwa cikin Na’ibawa, karamar hukumar Kumbotso.
Tuni dai Fatima da iyayenta suka maza suka fidda bidiyon Fatima dauke da kumburarriyar fuska da kuma raunika a jikinta da nufin su boye laifin ‘yarsu da cewa wai mijinta na azabtar da ita ne, kuma dalilin cin zarafin da ya ke yi mata ne ma ya sanya ta dauki wuka ta daba masa.
Tuni dai jami’an ‘yan sanda suka cafke Fatima, wacce dalibar shari’a ce a jami’ar Bayero.
Amma a wani taron manema labarai da Hussaini Sa’id ya yi, Hussaini ya zargi matarsa Fatima da neman maza, sannan ya musanta zargin cewa yana dukanta.
“Na kama matata tana rawar batsa a falo na kuma tana daukar rawar a wayarta tana turawa samarinta.
“Na fadawa mahaifiyarta abinda na samu matata tana yi, amma sai mahaifiyarta ta rokeni da kar na bari yayar matata da kakarta su san abinda ke faruwa, domin sanin nasu zai iya ja musu bata sunan iyalisu gaba daya.
“Haka kuma na taba tunkarar daya daga cikin samarinta wanda take turawa sakon murya ta kafar sadarwa, amma sai ya nuna min cewa Wallahi shi bai ma san matar aure bace.
“Wannan daya daga cikin sakonin murya sama da guda 30 da nake da su a matsayin shaida (ya kunna sautin sakon murya) wadanda matata ta aikawa wannan saurayin nata.
“Ina da shaidar yadda matata ta gayyaci saurayinta daga Abuja da kuma yadda suka sheka aya a wani dakin otal a Bompai wanda zai bayyana har sunan otal din nan gaba. Ta aikata wannan badala ne a ranar 26 ga watan Afrilun, 2016, a lokacin kuma tana da aure. Ta shiga dakin otal din da misalin karfe 10:13 na safe kuma ta kasance a dakin har zuwa karfe 12:16 na rana. na’urar daukar hoto na otal din ta dauki wannan abu da na ke fada muku.
“A dai wannan rana, wacce ranar Juma’a ce, na kama matata tana shaye-shayen miyagun kwayoyi, inda ta hada Shisha da wasu kwayoyin ta yi ta zuka. Ko a watan azumin da ya gabata ma sai da ta yi kokarin halaka ni ta hanyar sanya min guba a abincina. Ina da shaidar wainar kwan da ta soya min ta saka min guba a ciki.
“A lokacin da matsalolin matata ya zama ya fara wuce hankali, sai muka bukaci da mu ga Dakta Bashir Umar, babban limamin masallacin Juma’a na Al-Furqan, Kano, wanda fitaccen malami ne kuma wanda ke da kwarewa a harkar nasiha ga ma’aurata, domin ko watakila ya taimaka wajen busawa aurenmu numfashi.
Mun je wajen Dakta Bashir ne tare da matata, da mahaifiyarta da kuma yayanta a motata, kuma na zayyana masa dukkan abinda ke faruwa a tsakaninmu da ita har neme-nemen maza da ta ke yi zuwa su shan kwayoyi, kuma ta amsa laifukanta a gaban Dakta Bashir din.

“Amma kuma sai ga shi a wannan rana da muka je wajen Dakta Bashir, bayan mun dawo sai na karbe wayarta, wanda da shi ne ta ke aikawa samarinta hotunan tsiraicinta, shi ne ta yi yunkurin halaka ni da wuka bayan na kwanta barci. Ta yi hakan ne ta hanyar debo wukake har guda biyu daga kicin dinmu, inda ta zo ta zauna kusa da ni a kan gadon da nake barci, sai kuwa ta daga wuka ta farko ta daba min a gefen cikina ta zare wukar ta jefa ta a bayanta.

“Ina farkawa cikin tsananin ciwo sai na ga ta sake daga wata wukar za ta daba min, sai na rike wukar, dalilin da ya samu na samu wannan raunin da ke hannuna.

“Ta fizge wukar ta sake yunkurin sake daba min amma sai na kauce, dalilin da ya sanya wukar ta nutse a cikin katifarmu. A wannan lokaci ne fa na mike muka fara kokawa da ita ina kokarin karbe wukar da ke hannunta, a cikin haka har ta cije ni, inda ni kuma na sa ragowar karfin da nake da shi na tunkudeta ta fadi kan dirowar da ke cikin dakin kafin ta fadi kasa daga baya, wanda shi ne ya yi sanadiyyar kumburar fuskarta.

“Amma batun wai kokawa muka yi da ita a kicin ba komai bane face karya muraran. In aka duba inda jini ya zuba za a ga daga dakin kwananmu ne zuwa falo.

“A saboda haka ina kalubalantar iyaye da ‘yan uwan Fatima da su kawo duk wata shaida da suke da ita na cewa ina dukan Fatima a kowace rana, Bidiyon da suke ta yadawa na kumburin fuskar Fatima na wannan rigimar ce.

“Lawwali, abokina, shi ne ya taimaka ya kaini asibiti a daren. Ko da na bude idona ina cikin kunci sai na ga fuskar surukata (mahaifiyar matata) a kaina, nan da nan na yi mata kashedi da kar ta kuskura ta taba ni. Abokina Uztaz shiada ne.

“Nan na fara fada wa surukata cewa na fada miki irin miyagun halin da ‘yarki take yi na neman maza da yunkuri saka min guba a abinci, amma baki dauki wani mataki ba… Nan fa sai surukata ta far min alamar na yi shiru na daina magana kar na tona musu asiria idon duniya.

“Kafin surukata ta bar asibintin sai da ta nemi umarni daga abokina Ustaz na cewar tana so ta yi tattaunawar sirri da ‘yarta.

Hussaini ya ci gaba da cewa, labarin wai yana cin zarafin Fatima ta hanyar yi mata dukan tsiya kullum, shiryayyen labari ne a kokarin boye gaskiyar lamari da iyayen Fatima suke so su shirya kamar yadda ya faru a lamarin Maryam Sanda a Abuja.

“Shiryayyen bidiyo da wasu bayanai na cewa wai ian shaye-shaye duk wani tsari ne da aka bijiro da shi don al’umma ta tausayawa Fatima ni kuma laifin ya zama nawa duk kuwa da ni ta soka da wuka.

Hussaina ya bayyanawa manema labarai yadda ya dinga kai karar Fatima ga iyayenta  ta hanyar tura musu irin hotuna da take aikawa samarinta ta WhatsApp. Ni ma ina turawa iyayen nata ta WhatsApp hotunan tsiraicinta da ta ke turawa maza, kuma ina da wannan harkalla ta tura musu da na yi a wayata da ma abubuwa da suka fada a lokacin da na tura musu.

Hussaini ya bayyana cewa bai taba sanin cewa Fatima bata da halin kwarai ba kafin su yi aure kuma ko bayan da suka yi auren ma sai daga baya ya gano haka.

Ya kuma karyata zargin da ake yi na cewa wai auren dole aka yi wa Fatima. Hussaini ya ce ko ana gobe za a daura aurensu sai da mahaifinta ya sake tambayarta cewa wannan ita ce damarta ta karshe na zaben miji, shin tana son wanda za a daura aurensu a gobe, ta kuma amsa da cewa tana so.

®Alummata


Share this


Author: verified_user

0 Comments: