Labarai

Masu uwa a gindin murhu: An damke makasan diyar shugaban kungiyar Yarbawa Afenifere

Kwanaki uku da kashe diyar shugaban kungiyar Yarbawa, Afenifere, Pa Reuben Fasoranti, hukumar yan sandan Najeriya ta sanar da damke wadanda ake zargi da kashe Funke Olakunrin. Kakakin hukumar yan sandan jihar Ondo, Mista Femi Joseph, ya laburta hakan ne ranar Litinin. A cewarsa, gamayyar jami’an tsaro masu sintiri ne suka afka cikin daji a Ore dake jihar Ondo inda suka samu nasarar damkesu. Kakakin ya ce ba’a bayyana fuskokinsu ba amma za’ayi hakan ba da dadewa ba kuma ana cigaba da gudanar da bincike.

 A bangare guda, Kungiyar Fulani Makiyayan ta Najeriya (MACBAN) ta yi Alla wadai tare da nesanta kan ta daga kisan Funke Olakunrin, diyar shugaban kungiyar ‘yan kabilar Yoruba (Afenifere), Dattijo Reuben Fasoranti. A wani jawabi da ta fitar ranar Asabar a Abuja, mai dauke da sa hannun sakarenta na kasa, Baba Ngelzarma, kungiyar MACBAN ta mika sakon ta’aziyya ga Fasorati a kan rasuwar diyarsa. Ya ce marigayiyar ta mutu ne ranar Juma’a sakamakon harbinta da da wasu ‘yan bidiga suka yi a kan hanyar Kajola zuwa Ore a jihar Ondo kamar yadda rundunar ‘yan sanda ta bayyana. Ngelzarma ya ce, “Muna mika sakon ta’ziyyar mu ga dangin marigayiyar.”

Ya kara da cewa kungiyar MACBAN ta yi matukar mamakin yadda wani bangare na kafafen yada labarai da wasu marasa kishin kasa ke kokarin amfani da batun kisan marigayiya Funke domin rura wutar rikicin kabilanci.

® Legit

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button