Saturday, 27 July 2019
Masu gari: 'Yar gidan Gwamna Ganduje ta gwangwaje Ado Gwanja da kyautar tsaleliyar mota

Home Masu gari: 'Yar gidan Gwamna Ganduje ta gwangwaje Ado Gwanja da kyautar tsaleliyar mota
Ku Tura A Social Media
Diyar Gwamna jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Balaraba Ganduje, ta yiwa fitaccen mawakin nan Ado Gwanja wata gagarumar kyauta - Balaraba ta bai wa mawakin kyautar wata tsaleliyar mota kirar kamfanin Honda Accord baka - Mawakin ya wallafa hoton motar ne a shafinsa na Instagram inda ya bayyana cewa wannan kyauta ta fito daga wajen Balaraba ne Diyar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Balaraba Ganduje, ta yiwa fitaccen mawakin matan nan kyautar wata dankareriyar bakar mota kirar Honda Accord. Ado Gwanja ya wallafa hoton motar a shafinsa na Instagram, inda ya ce;

 "Alhamdulillahi wannan kyautar ta zo mini daga Balaraba, don ku kara tabbatar da cewa mun bi gidan hallaci, ni ke da uwar gaske madalla da kulawa Hajiya Balaraba," in ji Ado Gwanja. 

 Wannan kyauta dai ba ta zo da mamaki ba, idan zaku tuna Ado Gwanja yana daya daga cikin manyan mawakan jihar ta Kano da suka yi gwamna Ganduje a zaben da aka gabatar a farkon wannan shekarar a jihar ta Kano. Ko lokacin da aka dinga rade-radin cewa gwamna Ganduje zai sha kasa a lokacin zaben, hakan bai hana mawakin daina wallafa hotunan gwamnan a shafukansa na sada zumunta ba. Hakan ne yasa ake yi masa kallon dan a mutun gwamna Ganduje.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: