Sunday, 14 July 2019
Lalata da karamin yaro: Kotu ta yanke wa malamar makaranta hukuncin daurin shekara 20

Home Lalata da karamin yaro: Kotu ta yanke wa malamar makaranta hukuncin daurin shekara 20
Ku Tura A Social Media
Kotu ta yanke wa wata malamar makaranta, Brittany Zamora, hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari bayan an gurfanar da ita bisa tuhumar ta da aikata lalata da dalibi mai karancin shekaru.

Zamora, wacce tuni aka dade da kora daga aiki, ta amsa laifin aikata halayyar da ba ta dace ba da dalibinta mai shekaru 13.
Ta amsa laifukan tuhuma 10 da ake yi mata da suka hada da cin zarafin karamin yaro da nuna masa abubuwa marasa dace wa da suka shafi jima'i.
Asirin malama Zamora, mai shekaru 28, ya tonu ne bayan mahaifiyar dalibin; dan aji shida a wata makarantar firamare 'Las Brisas Academy' da ke Arizon a kasar Amurka, ta ga wasu sakonni da basu dace ba a wayar yaron.
Tun a shekarar 2018, hukumar makarantar 'Las Brisas Academy' ta kori malama Zamora, matar aure, daga aiki bayan ta amsa cewa ita ce ta aika wa yaron sakonnin waya na batsa.
Iyayen yaron sun shaida wa masu gabatar da kara cewa suna bibiyar wayar hannu ta yaronsu ta hanyar amfani da wata manhaja.

"A daya daga cikin sakonnin da Zamora ta aika wa yaron ta rubuta cewa ta na son dalibin mai shekaru 13 ya ke saduwa da ita kullum ba tare da wani shinge ba.
"Shi ma yaron na aika mata sakonnin da ke nuna cewa ya na jin dadin abinda malama Zamora ke aikata wa da shi tare da nuna jin dadinsa," a cewar masu gabatar da kara.
A ragowar sakonnin da suka yi musaya, Zamora da dalibin kan aika wa junansu hotunan tsiraici tare da sakonni masu motsa sha'awa.
Dalibin ya shaida wa iyayensa cewa alaka ta fara kullu wa tsakaninsa da malama Zamora bayan ta fara aiko masa sakonni nuna cewa ta na kwadayinsa da aiko masa hotunanta na tsiraici.

Ya kara da cewa shi da malama Zamora kan yi lalata a cikin motar ta da kuma cikin wani aji da sauran dalibai ke labe wa, su na leko wa.

® Legit

Share this


Author: verified_user

0 Comments: