Thursday, 11 July 2019
Ke duniya: Wani malami ya kori wata budurwa 'yar bautar kasa daga makarantarsa bayan taki amincewa yayi zina da ita

Home Ke duniya: Wani malami ya kori wata budurwa 'yar bautar kasa daga makarantarsa bayan taki amincewa yayi zina da ita
Ku Tura A Social Media
Wani labari da ya bazu a shafin sada zumunta na Twitter ya nuna yadda wani shugaban makaranta ya kori wata 'yar bautar kasa saboda taki yadda ya kwanta da ita

- Budurwar ta bayyana cewa mutumin yayi mata alkawarin gidan kwana da abinci da kudin kashewa, amma fa idan za ta yadda ya dinga kwanciya da ita

- Bayan ta nuna masa cewa baza ta yadda ba, sai ya koreta kuma yayi mata barazanar cewa zai kira hukumar NYSC ya sanar dasu cewa ita ce ta nuna bata son makarantarsa

Wata 'yar bautar kasa da aka tura ta garin Port Harcourt dake jihar Ribas domin gabatar da bautar kasarta na shekara, ta bayyana yadda shugaban makarantar da aka tura ta ya kore ta, saboda kawai taki yarda ya kwanta da ita.

Mutumin da ake tunanin shine shugaban makarantar ya yiwa budurwar alkawarin zai bata gidan kwana, abinci da kudin kashewa, amma kuma yaki sanya hannu akan takardar da zata nuna ya karbe ta, inda ya bayyana mata cewa dole sai ta kwanta dashi tukunna kafin ya sanya hannu.


Wata mai amfani da shafin sada zumunta na Twitter, ita ce ta wallafa labarin a shafinta na, inda ta kara da cewa shugaban makarantar ya yiwa budurwar barazanar cewa zai kira hukumar NYSC ya bayyana musu cewa ita ce taki yarda da makarantarsa.

Labarin ya fito fili ne bayan 'yar bautar kasar ta kira wata kawarta tana bayyana mata abinda ya faru ta na kuka, shine ita kuma kawar ta ga cewa ya kamata ta sanar da duniya ainahin abinda yake faruwa da 'yan bautar kasa musamman mata, wanda kullum ake yi musu barazanar kora idan basu bada kansu an kwanta dasu ba.

®Legit

Share this


Author: verified_user

0 Comments: