Wednesday, 3 July 2019
Karin Bayani Akan Auren Da Aka Yi A Facebook - Dr Muhammad Rabiu R/Lemo

Home Karin Bayani Akan Auren Da Aka Yi A Facebook - Dr Muhammad Rabiu R/Lemo
Ku Tura A Social Media

Wasu suna cewa ai ta wakilta wani ya zamar mata waliyyi!. To ba hakkinta ba ne ta ayyana waliyinta, matukar wadanda shari'a ta ayyana suna nan, kuma ba sabanin addini aka samu ba tsakaninta da su, musulmai ne kamar yadda take musulma, kuma ma koda babu waliyyanta duk sun kare, ko sun saba a addini tsakaninta da su, ita musulma ce su kafirai ne, to shugaban musulmi shi yake da hakki ya aurar da ita. Idan kuwa babu waliyyan, kuma babu shugaban, to a nan ne wasu malamai suke ganin zata iya wakilta wani ya zamar mata waliyyi.

Sannan wani abu mai mahimmanci da ya kamata mu gane, shi ne : Walittaka ga mace hakki ne da shari'a ta tsara wadanda suke da shi, kawai dai malamai sun yi sabani akan waye za a gabatar a cikinsu, uba ne ko da, don haka ma malamai suka yi sabani idan wanda ya fi cancanta ya zama waliyyin mace yana nan, sai wanda yake bai kai shi ba ya aurar da ita, ba tare da izinin wancan ba, shin auren ya yi, ko bai yi ba, to ina ga ita macen da ba hakkinta ba ne walittakar kanta, ta ayyana wani alhali waliyyanta suna nan, basu suka ayyana shi ba, haka nan shugaban musulmi ko Alkali da yake wakiltar shugaba yana nan, ba shi ya ayyana shi ba. Don haka wannan aure bai dauru ba, sai dai abin da suka yi ba daidai ba ne, don wasa ne da addini, su tuba su nemi yafiyar Allah, don al'amuran addini ba wasa a ciki.

Amma da a ce waliyyinta ne ya aura masa, shi kuma ko wakilinsa ya karba, da niyyar za a bayar da sadaki, kuma aka samu shaidu, to aure ya dauru, basu da damar su zo su ce wasa suke yi, don ba a wasa da daurin aure. Allah ne Masani.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: