Tuesday, 23 July 2019
Jerin ministoci 10 da suka samu dawowa majalisar Buhari

Home Jerin ministoci 10 da suka samu dawowa majalisar Buhari
Ku Tura A Social Media
Bayan dogon jira da zuba idanu da yan Najeriya suka yi wajen so ganin wadanda za su kafa majalisar dhugaban kasa Muhammadu Buhari na biyu, a yau Talata, 23 ga watan Yuli, Shugaban kasar ya tura sunayen ministocinsa na Next Level ga majalisar dattawa domin tantancewa.

Shugaban kasar dai ya tura sunayen mutane 43 zuwa majalisar domin tantancewa. Don haka muka yi amfani da wannan dama wajen zakulo maku sunayen tsoffin ministocinsa guda 10 da suka samu dammar komawa a karo na biyu.


Ga sunayensu kamar haka:

1. Ebonyi: Dr Ogbnayya Onu - Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha

2. Edo - Osagie -

3. Adamawa: Muhammad Bello - Tsohon Minsitan Abuja

4. Anambara - Chris Ngige - Tsohon Ministan Kwadago

5. Bauchi - Adamu Adamu - Tsohon Ministan Ilimi

6. Enugu: Geofreey Onyeama -

7. Kaduna: Zainab Shamsuna - Tsohuwar Ministar Kudi

8. Kwara: Lai Mohammad - Tsohon Ministan Watsa Labarai

9. Lagos: Babtunde Fashola - Tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje

10. Rivers: Rotimi Amaechi - Tsohon Ministan Sufuri

Share this


Author: verified_user

0 Comments: