Monday, 1 July 2019
INNALILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJI'UUN : Labari MUni ,mafi Tayar Da Hankali Daga Gurin Musulma Amina Muhammad

Home INNALILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJI'UUN : Labari MUni ,mafi Tayar Da Hankali Daga Gurin Musulma Amina Muhammad
Ku Tura A Social Media

Labari mafi muni, mafi tayar da hankali da girgiza zuciya, wanda Wallahi ko a mafarki banyi tsammanin hakan zai faru ba daga gurin Musulmi ko Musulma

Mataimakiyar sakataren majalisar dinkin duniya Hajiya Amina Muhammad 'yar uwarmu Musulma, itace ta wallafa sanarwa a shafinta na Twitter tana mai cewa lokaci yayi da zata jagoranci neman bayar da 'yanci a duk kasashen duniya ga 'yan Luwadi, da 'yan Madigo, da masu zina da dabbobi da sauransu, wadanda a kungiyance ake kiransu da "Lesbian, Gay, Transgender, Bisexual and Queer" (LGTBQ).

Muna raye a duniya wannan abin zai faru? innalilLahi wa innaa ilaiHi raji'uun!, Malamai aiki ya sameku, dole ku tashi ku fara wa'azi da khudubah akan abinda wannan matar tayi alwashin aiwatarwa a duniya, duk wani Malami ko shugaba mai fada aji da yayi shiru akan wannan mummunan kuduri wallahi yaci amanar al'ummah kuma yaci amanar Musulunci

Amina munyi hannu riga dake, wallahi babu mu babu ke har abada matukar baki janye wannan mummunan kuduri ba, domin kin taro fada da Allah (SWT)
Muna dauke da sako zuwa gareta, duk wanda yake da kusanci da ita muna neman alfarma ya isar mata da sakon da zamu wallafa

Yaa Allah mun kawo karansu gareKa, Ka isar mana tsakaninmu da su!

Share this


Author: verified_user

0 Comments: