Sunday, 7 July 2019
In Dai Haka Sana'ar Fim Din Hausa Take Allah Wadaran Ta Wallahi

Home In Dai Haka Sana'ar Fim Din Hausa Take Allah Wadaran Ta Wallahi
Ku Tura A Social Media

Yan Kannywood Allah ya tsine ma wannan arzikin da kuke ikirarin kuna samu da wannan sana’ar taku, in dai baza ku taimaki junan ku ba, wannan sana’ar taku sana’ar banza ce.

Ina Directors da masu Hannu da shunin cikin ku suke, kuna ta mutuwa bakwa taimakon Junan ku, sai kyalkyalin banza da hofi kuke da kuma bama karuwai kudi domin ku burge duniya, ku ga yan iska.

Kuga wannan bawan Allah Sani Idris (MODA) an gwantule masa Kafa kuna kallo, ba acting bane da gaske an yanke masa Kafa saboda laluran da ta same shi, sai dai wannan ya kawo masa Lemu da ayaba ko abarba ya wuce, uwarku zaiyi da wannan abubuwan.

Tin kafin a haifi wasun ku, wannan mutumin yake dirama domin fadakar wa, ba bata tarbiyya irin taku ta yanzu ba. Wanda basu mutu a cikin ku ba, toh ku nemi Sana’a kafin rashin lafiya ya riske ku.

Kun iya zuwa saudiyya domin kuma Allah riya, amma Kar ku manta Allah zaiyi maganin ku, mutanen banza kawai.

Wallah kunji kunya sosai, MODA Allah ya yafe maka kurakuren ka, ya baka lafiya.

Muawiyya Maidankali Shuaibu

Share this


Author: verified_user

0 Comments: