Tuesday, 9 July 2019
Har Yanzu Babu Wacce Nake So Da Aure kamar Jaruma Nafisa - Zaharadden Nasir (Navy)

Home Har Yanzu Babu Wacce Nake So Da Aure kamar Jaruma Nafisa - Zaharadden Nasir (Navy)
Ku Tura A Social Media


Wani matashin Jami'in Sojin ruwa (Navy) ya kuma tabbatarwa da duniya cewar har yanzu babu wata mace da yake so duk duniya kamar Jarumar masanaantar Shirya fina finan Kanyywood, Nafisa Abdullahi, wacce ake yima lakabi da sai wata rana.

Ya ce ya dauki tsawon Shekaru yana farautar zuciyar Jarumar amma har yanzu taki bashi dama.

Jami'in mai suna ZAHARADDEEN NASIR, wanda ya kwashe shekaru yana aiki da hukumar Sojin ruwa ya kara da cewa shi da Aure yake son Nafisa Abdullahi, yanzu haka da zata bashi dama ko shakka baya yi zai bayar da sadaki a daura musu Aure.

Har ila yau ZAHARADDEEN NASIR, ya ce duk lokacin daya ga ana suka ko zagin Jarumar baya jin dadi ko kadan, yana mai cike da farin ciki idan yana kallon hotunan ta ko Fina finan ta.

Ya bayyana haka ne ga wakilin Jaridar Dimokuradiyya, Shuaibu Abdullahi a wata tattaunawa ta wayar tarho ya ce yana mai rokon Jarumar ta duba girman Allah ta bashi damar Auren ta.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: