Monday, 8 July 2019
Gaskiyar Magana Akan Kama Mawaki Isah Ayagi

Home Gaskiyar Magana Akan Kama Mawaki Isah Ayagi
Ku Tura A Social Media

A 'Yan kwanakin nan wata magana ta yadu a kafafen sada zumunta na cewa an kama shararren mawakin Hausa wato isah ayagi, Yayinda Jama'a ke zargin an kamashi ne saboda yayi wata Sabuwar wakar siyasa wacce take nuna Cin zarafi ga Gwamnan jihar kano Ganduje.

Sakamakon Wannan Jita Jita data yadu a Gari  hakan ne yasa wakilanmu suka Tuntubi mawakin kai tsaye domin jin Gaskiyar Magana.

Mawaki Isah Ayagi Ya Shaidawa wakilan mu cewa wannan al'amari ba Gaskiya bane hakan bata faru dashi ba, Saidai yana Zargin ko hakan ta faru da wani mawakin ne sai wasu sukaji Labarin ba'a daidai ba shiyasa suke zaton Ko shine.

Ya Kara da cewa nima dai haka kawai natashi naji anata kirana a waya wai an kamani dafarko Na dauki abun wasa saikuma danaga Kiran wayar yayi yawa sannan na fahimci maganar tayi nisa.

Mawakin Ya kara dacewa yakamata mutane su dinga jin sahihancin Labari kafin su yadashi domin yada labarin karya laifi ne a addinan ce dakuma dokar kasa.

A Karshe Isah ya mika godiya ga Masoyan sa akan Irin Soyayya Da kulawar dasuke nuna masa tareda yi musu albishirin Zafafan kundin wakokin sa Guda 2 dazai saki nan Bada jimawa ba Masu Taken "SABON LABARI & DAUKAR AMARE"

Share this


Author: verified_user

0 Comments: