Friday, 12 July 2019
Dangote Ya Sayi Kowacce Kwallon Najeriya Dalar Amurka Dubu Hamsin $50,000

Home Dangote Ya Sayi Kowacce Kwallon Najeriya Dalar Amurka Dubu Hamsin $50,000
Ku Tura A Social Media


Hamshakin Dankasuwa kuma mutum mafi arziki a nahiyar Afirka Aliko Dangote, ya sha alwashin sayen kowacce kwallo daya da kungiyar kwallon kafar Najeriya ta zura a akan Dalar Amurka $50,000 daidai da Naira Miliyon 18,000,525.19, a wasan da zata fafata a rukunin kusa da karshe wato Semi Final

Matakin na Dangote na daga cikin karawa kungiyar kwallon kafar Najeriya kwarin guiwa domin ganin ta ciyo kofin nahiyar Afirka wanda yanzu haka yake gudana a kasar Egypt.

Sai dai Wannnan mataki na Dangote ya janyo kace nace a tsakanin al'umma, yayinda wasu ke yabon matakin, a gefe guda kuma wasu kushe matakin suke inda suke cewar, kudin yafi dacewa ayiwa yan gudun hijira da mabukata tallafi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: