Friday, 5 July 2019
Bana goyon bayan wasan da Nicki Minaj zata yi a kasar Saudiyya-Maryam Booth

Home Bana goyon bayan wasan da Nicki Minaj zata yi a kasar Saudiyya-Maryam Booth
Ku Tura A Social Media

A jiyane labarin cewa tauraruwar mawakiyar kasar Amurka, Nciky Minaj zata yi wasa a kasar Saudiyya ya bayyana inda dama, musamman musulmai sukai ta bayyana mabanbanta ra'ayoyinsu akan wannan lamari,

Itama tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth ta bayyana ra'ayinta akai.

A sakon data fitar ta shafinta na Twitter, Maryam ta bayyana cewa,

Salamu alaikum 'yanuwa maza da mata ina da tambaya. Menene ra'ayinku akan wasan da Nicki Minaj zata yi a kasar Saudiyya?

Ina son wakokinta amma bana goyon bayan wasan da zata yi a kasa me tsarki.Wasu dai sun bayyana cewa basu ga laifin hakan ba tunda ba a cikin garin makka ko Madina zata yi wasan ba a jedda ne.

Wasu kuwa sunce wasan na Nicki Minaj kwata kwata be dace ba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: