Wednesday, 3 July 2019
Babu sauki ko kadan mulki a kasar nan – Shugaba Buhari

Home Babu sauki ko kadan mulki a kasar nan – Shugaba Buhari
Ku Tura A Social Media
Shugaban kasa Muhammad Buhari yace akwai wahala sosai wajen gabatar da nasarorin gwamnatinsa ga yan Najeriya, inda ya daura laifin akan manyan yan Najeriya da ke sanya ra’ayin kansu a ciki.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da mambobin kungiyar Buhari Media Organisation (BMO) suka ziyarce shi a fadar shugaban kasa a ranar Talata, 2 ga watan Yuli.

“Ba karamin aiki bane gabatar da nasarorin wannan gwamnatin. Amman dole muyi abubawa yanda ya kamata. Idan muka sha alwashin kawo canji, dole mu aikata hakan, ba tare da la’akari da bin ra’ayin wasu ba. Dole mu gabatar da manufofin barin hanyoyin baya.

“Cimma wadannan alkawarin uku ya zama dole mu kai Najeriya zuwa mataki na gaba. Ina tabbatar muku da cewa na yanke shawarar sauke wadannan alkawaran. Idan muka tafi, Najeriya zata gyaru fiye da yanda muka same ta.


“Sako guda daya dake da muhimmanci gare ni, wanda nake bukatar ku yada, shine cewa na jajirce wajen ganin na kawo karshen kalubalen tsaro da muke fuskanta a matsayin kasa, tare da mayar da Najeriya kasa mai zaman lafiya da cigaba.”

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya na bukatar gwaraza a gwamnatinsa wadanda za su tsaya su yi aiki tukuru idan har ya na so ya ga an kai kasar zuwa ga ci a mulkinsa.

A Ranar Talata 2 ga Watan Yuli, Buhari ya fadawa wasu Magoya bayansa da ke karkashin kungiyar BMO cewa tafiyarsa sai da gogaggun mukarraban da za su dafa masa domin cika alkawura.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: