Saturday, 6 July 2019
An Yankewa Fitaccen Ɗan Wasan Hausa Ƙafa Sani Mode

Home An Yankewa Fitaccen Ɗan Wasan Hausa Ƙafa Sani Mode
Ku Tura A Social Media


Sani Moɗa na ɗaya daga cikin manyan fitattun jarumai da su ka yi tashe a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta (Kannywood) musamman fannin barkwanci da abin ban dariya.

Biyo bayan wata doguwar jinya da ya yi, yanzu haka an yanke masa kafa ɗaya, ya na kuma kwance a Asibiti ƙarƙashin kulawar Likita.

 wannan Hotuna ne daga shafina ɗaya daga cikin Jaruman masana'antar Ladidi Abdullahi, inda ta wallafasu a shafinta na Facebook, jim kaɗan bayan da ta ziyarce shi a Asibitin da ya ke kwance.


Indai jama'a ba su mance ba, ko a kwanakin baya an yi ta baza labarin Mutuwar Sani Moɗa amma daga bisani ya fito ya musanta.

Inda yanzu kuma ta bayyana cewa ya yi fama ne da rashin lafiya, kuma har ta kai ga zama sanadiyar rasa ƙafarsa guda ɗaya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: