Wednesday, 24 July 2019
An kulle wani gidan talabijin na Musulunci a kasar Ingila saboda sukar 'Yan Luwadi

Home An kulle wani gidan talabijin na Musulunci a kasar Ingila saboda sukar 'Yan Luwadi
Ku Tura A Social Media

Za a kwace lasisin wani gidan talabijin na Musulunci dake kasar Birtaniya, bayan sun yi wata magana akan 'yan luwadi da matsafa.
Peace TV, wadanda suke zaune a Dubai, an kama su da laifin nuna wasu shiri guda hudu wadanda suka sabawa doka, kuma ake musu kallon masu neman tada zaune tsaye, jaridar Daily Mail ita ce ta ruwaito.

Tashar wacce suka gabatar da shirye-shriyensu akan koyarwar Musulunci, sai dai a wani shiri wanda daya daga cikin Malaman mai suna Imam Qasim Kha ya ce Aladu sun fi 'yan luwadi daraja, kuma kamata yayi a dinga kashe matsafa.

Shirin ya nuna yadda mutanen da suke aikata wannan dabi'a suke mutuwa saboda cutar da suka dauka saboda luwadi, haka kuma ya ce luwadi wata dabi'a ce da shaidan yake sanyawa masu yinta soyayyarta a cikin zuciyarsu.

A cewar Imam Qasim Khan, "Yanzu sun shigo da wata doka, sabuwar doka wacce hankali ba zai dauka ba, dokar da take goyon bayan 'yan luwadi, har ma take basu goyon bayan auren junansu.

"Ko dabbar da ta fi kowacce rashin daraja, wacce addinin Musulunci yayi hani da amfani da ita, wato Alade, ba za ka taba ganin jinsin alade maza suna saduwa da junansu ba." Wannan hauka ne.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: