Friday, 5 July 2019
An gurfanar da wani Zakara a gaban kotu, saboda yana damun mutane da cara

Home An gurfanar da wani Zakara a gaban kotu, saboda yana damun mutane da cara
Ku Tura A Social Media
An kai wani zakara da yake damun mutane da cara kara wata babbar kotu a kasar Faransa

- Zakaran mai suna Maurice ya gurfana a gaban kuliya, bayan wasu ma'aurata sun kai karar cewa yana damunsu da kuka a lokacin da suke hutawa

- Mai zakaran ta bayyana cewa wannan al'adace ta kowanne zakara ya dinga yin cara, saboda haka bata ga dalilin tada jijiyar wuya da ma'auratan suke yi ba

An fara sauraron wata kara a wata babbar kotu dake kasar Faransa akan wani zakara mai suna Maurice, bayan wasu ma'aurata sun kai shi kara akan cewa yana takura musu da kuka.

Zakaran wanda kukansa yake takurawa makwabtan gidan da yake, ya tada hankalin mutanen dake makwabtaka dashi, inda suka garzaya zuwa kotu domin yin shari'a dashi.

Wasu tsofaffin ma'aurata ne suka zargi zakaran da shiga hakkinsu, inda suka bayyana cewa cararsa na damunsu, a wani tsibiri da suke zaune na Oleron dake kasar Faransa.


A kokarin da mai zakaran take yi na kare zakaranta, ta bayyana cewa Maurice yana yin abinda aka san kowanne zakara nayi ne.

Masu kai karar zakaran da shi zakaran basu samu damar halartar zaman kotun ba a ranar farko da aka fara sauraron karar.

Sai dai kuma zakaran wanda yayi kaurin suna a yankin, ya samu goyon bayan mutane masu kiwon irinsa, inda suka yi dafifi zuwa kotun.

A yanzu haka dai kotu ta bayyana watan Satumba a matsayin watan da zata yanke hukunci na karshe game da zakaran da masu kararshi.

® Legit

Share this


Author: verified_user

0 Comments: