Monday, 8 July 2019
Ahmed Musa Ya Fadi Abinda Zaiyi Idan Munka Lashe Kofin AFCON

Home Ahmed Musa Ya Fadi Abinda Zaiyi Idan Munka Lashe Kofin AFCON
Ku Tura A Social Media
Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa na Super Eagles, Ahmed Musa, ya bayyana cewa ya na harin lashe gasar cin kofin Nahiyar Afrika da a ke bugawa ne saboda Marigayi Stephen Keshi.

Babban ‘Dan wasan ya nuna sha’awarsa na sake lashe kofin na Afrika a wannan shekarar kamar yadda ya taki nasara a 2013 lokacin da Marigayi tsohon Koci Stephen Keshi ya jagoranci kasar.

Ahmed Musa ya bayyanawa CAF Online cewa babu abin da ya fi dadi kamar ‘dan wasan kwallo ya samu nasara da kasarsa. Super Eagles ta gaza zuwa gasa biyu na baya da a ka buga a Nahiyar.

Musa ya ce:

Idan mu ka lashe wannan gasam zan sadaukar da nasarar ne ga Marigayi Stephen Keshi wanda ya kasance kamar Mahaifi a wuri na. Ba abu bane mai sauki rashin mutum na musamman.”

Ahmed Musa ya ce ya shaku sosai da tsohon Kocin na Super Eagles, kuma shi ne ya ke taimakawa wajen tunzurasa wajen zama abin da ya zama.

‘Dan wasan gaban ya kara da cewa:

Akwai abubuwa sosai da na koya wajen sa (Keshi) a matsayinsa na ‘Dan Adam kuma Mai horaswa. Mu ‘Yan wasansa, mu na kewarsa. Kuma a matsayin mu na ‘Yan kasa, mu na cigaba da yi masa a addu’a. Zai yi kyau mu ci wannan kofin saboda shi.”

Tsohon ‘dan kwallon na Leicester City ya kuma bayyana cewa Najeriya ba ta tsoron kowace kasa a Gasar duk da ya san cewa babu kasar rainawa a Afrika. Musa ya ce za su yi iyaka bakin kokarinsu.
® Legit

Share this


Author: verified_user

0 Comments: