Tuesday, 2 July 2019
Abun Farin ciki Daga Kannywood An Sanya Mandu'in Nura M Inuwa A Jarabawar Neco 2019

Home Abun Farin ciki Daga Kannywood An Sanya Mandu'in Nura M Inuwa A Jarabawar Neco 2019
Ku Tura A Social Media


Masha Allah a madadin ceo Hausaloaded blog Abubakar Rabiu da mabiya ziyarar wannan shafi na taya shahararren mawakin nan nura m inuwa wannan cigaba daga sana'arsa.Daya daga cikin yaran nura m Inuwa ko ince abokin aikinsa Annur H Abnur tofa albarkacin bakinsa .

"Alhamdulillah!Ganin wannan tambayar a cikin jarabawar NECO ta 2019 ba karamin abun alfahari bane a garemu qasar Hausa baki daya.Dan idan mun duba zamuga ana nazarin waqoqin mawaqan daurin ne kawai amma ba a fiya duba abun da mawaqan yanzu sukeyi ba bare ma har a sakashi akan mizanin nazarin ADABI.Amma duba da irin baiwa,saqonni,fadakarwa,nishadantarwa,wa'azantarwa da ilimantarwa dake cikin waqonqin @nura_m_inuwa an tsundumashi cikin mawaqan da ake nazarin waqoqinsu a kasar Hausa.Allah ya qara Daukaka harshen  Hausa, Allah kuma ya qara yi mana jagora.Congratulations Sir. Ka cancanci piye da haka.Allah ya qara dauka da arzuki mai albarka. @nura_m_inuwa"

Share this


Author: verified_user

0 Comments: