Saturday, 8 June 2019
Yanzu Yanzu: Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi sun yi sulhu

Home Yanzu Yanzu: Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi sun yi sulhu
Ku Tura A Social Media
Akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa rikici tsakanin gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya zo karshe biyo bayan wata matsaya da aka cimma a daren ranar Juma’a a Abuja.

Da farko dai a ranar Juma’a Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga lamarin, biyo bayan kiran da aka yi kan ya sanya baki da kuma yawan kira daga dattawan arewa yayinda rikici tsakanin gwamnan da sarkin ke kara daga hakula a jihar.

Sanya bakin Shugaban kasa a lamarin na zuwa ne kwana daya kafin wa’adin da gwamnatin jihar ta dibar ma sarkin akan yayi bayani game da kudaden masarautar.

A taron sulhun da aka gudanar a daren ranar Juma’a a Abuja, gwamnan da sarkin sun amince sun janye takobinsu don ra’ayin Kao da kuma rage fargaba domin guje ma karya doka da oda.


Koda dai har yanzu babu cikakken bayani kan abunda ganawar ta kunsa, wata majiya abun dogaro ta bayyana cewa Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ne ya jagoranci ganawar wacce ta samu halartan yan tsirarun manyan mutane.

®Legit.ng

Share this


Author: verified_user

0 Comments: