Wednesday, 19 June 2019
Yan iska sun yi wa Oshiomhole da zababbun yan majalisar Edo dukan tsiya a Benin

Home Yan iska sun yi wa Oshiomhole da zababbun yan majalisar Edo dukan tsiya a Benin
Ku Tura A Social Media
Rikicin da ke faruwa a majalisar dokokin jihar Edo ya dauki sabon salo inda ya kai ga har an dabbatu

- Wasu yan iska sun far ma wasu zababbun yan majalisa da duka a majalisar dokokin jihar

- Daga cikin wadanda abun ya cika dasu harda Seidu, kanin Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole

Wani rahoto daga jaridar Nigerian Tribune ya nuna cewa wasu yan iska sun far ma zababbun yan majalisa 15, ciki harda Mista Seidu Oshiomhole mai wakiltan Etsako West 11 a majalisar dokokin jihar Edo.

Seidu ya kasance kani ga Kwamrad Adams Oshiomhole, Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa.

Majalisar dokokin jihar Edo na cikin rikici a yan kwanakin nan biyo bayan batun ballewar APC a jihar Edo.

Anyi gaggawan daaukar wasu daga cikin yan majalisar wadanda aka ce sun raunana sosai zuwa asibiti domin samun kulawar likita inda suke samun sauki.

A cewar rahoton, yan majalisa 15 da aka kai wa hari sun kasance magoya bayan Shugaban APC kasa, kuma an tattaro cewa ba a gayyace su zuwa wajen ratsar da majalisar dokokin jihar ba a ranar Litinin, 17 ga watan Yuni, inda mambobi tara suka zabi Frank Okiye a matsayin kakakin majalisa.


A lokacin rigimar, yan iska sun yi wa zababbun yan majalisar da suka sha alwashin kin amincewa da Okiye, dan kashenin Gwamna Godwin Obaseki a matsayin kakakin majalisa dukkan tsiya.

Wani hadimi na daya daga cikin yan majaalisar da ya nemi a boye sunansa, yace zababbun yaan majalisar na gaanawa a wani otel a babbar birnin jihaar, Benin lokacin da lamarin ya afku.

®Legit

Share this


Author: verified_user

0 Comments: