Saturday, 22 June 2019
Wata Mata Tayi Ma Mijinta Allurar Fiya Fiya, Bayan Sunyi Auren Soyayya (Hotuna)

Home Wata Mata Tayi Ma Mijinta Allurar Fiya Fiya, Bayan Sunyi Auren Soyayya (Hotuna)
Ku Tura A Social Media


Wakiliyarmu Murjanatu Sani Dabai

Wata Mata Mai Suna Hasiya Mustapha, Ta yi Yunkurin Kashe Mijinta Ahamed Baba Mohammed, Bayan sun Dade Cikin Soyayya Kafin suka yi Aure, ta hanyar yi masa Allurar Gubar Fiya-Fiya, a Wuyan sa.

Ita dai Wannan Baiwar Allah Kafin Auren su Jama'a sun Shedeta da Halin Kirki Mutuka, Amma Bayan Aurenta Sai ta Kama Kawance da Irin Matan nan da ake Kira Gida ko Mota, Ma'ana dai 'Yan Duniya.

Inda Shedan Ya Buga Mata Gangar nan Tashi mai Dan Karen Tsaki, a sakamakon Hudubar da Wadancan ƙawaye ƴan duniya suka Mata har ta kai ga sun zugata wai ta kashe Aurenta za su kai ta Abuja, inda za a Ba ta Miliyan daya, Alhali su Cikin su ba Mai Buhun Taki daya.

Bayan sun sami Nasara a kanta ne ita kuma ta sami Iyayenta ta ce Musu Ita fa yanzu ba ta son Wannan Mijin nata don haka Kawai a raba Auren iyayen nata sukaƙi tayi tayi amma suka ƙi yin hakan shine fa ta ɗauki nata Matakin.

inda ta ƙuduri a niyyar yin barazana da rayuwar Mijin ko yin hakan zai sa mijin ya saketa, har taje kasuwa ta siyo fiyafiya don ta yi wa Mijin Allura da Shi.

A Iya tunanin ta ko idan ta yi mishi Allurar fiyafiyar in ma bai mutu ba to in ya ji wahala zai saketa, Inji ta.

Wanda kuma ta Sami nasarar aiwatar da hakan Inda ta yi mishi allurar wanda Sanadiyar Hakan da ƙyar likitoci suka Ceto Rayuwar Shi, Yanzu Haka yana Kwance a Babban Asibitin Garin Jos, a Jihar Filato.

Da Fatan Allah Ya ba shi Lafiya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: