Tuesday, 25 June 2019
Wasu Abubuwa Guda 10 Da Mata Basu La'akari Dasu idan Suna Soyayya Na Gaskiya

Home Wasu Abubuwa Guda 10 Da Mata Basu La'akari Dasu idan Suna Soyayya Na Gaskiya
Ku Tura A Social Media


Tonga A U Abdul

A duk lokacin da kaga mace na cewa sai mai kaza da kaza zan aura bata fada kogin soyayya ba. Ga mace sake tsakiyar kogin soyayya babu ruwanta da yiwa Wanda take so ka'ida.
Dayawa daga cikin maza sunada tunanin cewa sai sunada wani abu na kyalekyale kamin mace ta so su Wanda ba haka abun yake ba.
Su fa mata shu'umai ne, idan kana tunanin zaka burgeta da mota sai mai Jaki yazo ya kasaka. Haka idan kana takama da kudi sai talaka yazo ya aureta. Kanaji kana gani da illiminka mace tana iya kinka tace jahili ne yayi mata. Ka sha kwalliyarka mai tsada wani da 'yan tsummokaransa ya kwacemaka budurwa, don haka ita mace da zaran kayi dace da zuciyarta to fa ka gama da ita.

Wasu na ganin cewa a wannan zamanin da ake ciki tamkar babu soyayya na gaskiya Wanda duk mai dauke da wannan tunanin a kwakwaluwarsa yana dakon kuskuren fahimta koda kuwa ya taba fadawa komar mayaudariya.  Akasarin kuskuren da maza sukeyi shine rashin tsayawa su yiwa budurwar da sukeso da sure kyankywan nazari kamin su fada soyayyya.

Wannan mukalar zai bayyanawa masu karatu musamman maza wasu abubuwan da basu tsolewa mata idanuwa ba  idan suna soyayya na gaskiya.

1: Mota Mai Tsada

Maza da dama sun dauka idan sun mallaki imota mai dan karen tsada shikenan sun mallaki soyayyar mace, wanda ba haka abun yake ba.
'Yan mata da dama suna amfani da samarinsu masu mota direbobinsu a fakaice Wanda da dama samarin basu fahimtar hakan. Soyayyansu na tashi ne a lokutan da suke da bukatuwa na abun hawa.

2: Kudi
Babu wanda bai son kudi ko kusanta da mau kudi musamman ma mata. Amma ita macen dake soyayya na gaskiya bata ganin mai kudi a mai kudi kamar yadda bata ganin talaka a mara kudi idan tana soyayya dashi.
Macen dake soyayya na gaskiya mai kudi na iya bata kyautan makudai taki karba, kamar yadda zata karba a wajen maikudi ko ta nemo ta baiwa talakan saurayinta.

3: Wasu Matan:
Idan kaji mace tana cewa bazata auri mai mata ba, bata samu wanda take so bane shi yasata fadin  hakan.
Idan mace ta kamu da soyayya duk yawan matan masoyinta gani take ita kadaice take mallakarsa duk da yake akwai wasu Matan da ba haka suka so ba.

4:Matsayi

Wasu mazan gani suke da zaran sun nunawa mace irin matsayinsu ko mukaminsu shikenan Zara fada soyayya dasu. Mata ba haka suke ba.
Mace na iya amfani da matsayinka ko mukaminka ta Gina saurayinda takeso dakai ba tare da ka fahimcin hakan ba kamin ka ankara sai dai kaji labarin aurensu.

5: Halitta-
Mace idan tana soyayya na gaskiya babu ruwanta da halittan mu ko jissinsa.
Zakaga kyankyawan mace tana matukar son mummunar namiji kuma tana alfahari dashi har cikin ranta.
Haka akwai mata masu soyayya da guragu, makafi, kurame ko bebaye.
Ana iya ganin bakar fata yana soyayya da balarabiya, indiya ko baturiya. It's mace muddin ta fada soyayya na gaskiya babu ruwanta da wadannan.

6:  Kabilanci:
Mata basa la'akari da yaren wanda suke soyayya dashi. Saboda hakan ne ake samun cudanyar harsuna a auratayya.

7: Yawan 'ya'ya:
Duk macen datake son namiji kamar yaddda yawan matansa bai dameta ba, haka ma yawan 'ya'yansa bai tsolemata idunuwa.

8: Shekaru:
Mace tsohuwa za aga ta matowa jikanta. Haka mace mai karancin shekaru za aga duk duniya babu Wanda take so da kauna irin sa'an kakanta. Mace mai soyayya na gaskiya babu ruwanta da tsufa ko yarintar wanda take so.

9: Nisa Ko Bambamci Gari:

Mace mai soyayyya na gaskiya babu ruwanta da Nisan dake tsakaninta da Wanda take so.

Mace tana iya soyayya da namiji da basu had a unguwa daya ba, basu hada gari daya ba, basu had a kasa daya ba bare kuma nahiya ko lardi guda ba. Kuma tayi soyayya dashi na gaskiya ba tare da ta ci amanarsa ba.

10: Akida Ko Ra'ayi:
Bambamcin akida na addini ko bambamci ra'ayi akan wani abu bai hana mace son namiji soyayya kuma na gaskiya.
Za aga 'yar wata kungiya na addini tana soyayya da wanda ba dan kungiyarta bane. Akwai wash matan ma da suke canji addini idan sun samu kansu a soyayya na gaskiya.

Wadannan sune wasu daga cikin abubuwan da mata basa la'akari dasu idan suna ciki a soyayya.
Saboda yadda mata suke shiga soyayya ba tare da la'akari da wasu mahimman abubuwa, suke Shiga matsala ko matsaloli irin na soyayyya.
Da fatan mata zasu nemi illimin sanin muhimman abubuwan da zasu yi la'akari dasu kami fadawa soyayya da namiji.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: