Wednesday, 5 June 2019
Wanda Ake Bi Bashin Ramadan Zan Iya sittan Shawwal ? - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano

Home Wanda Ake Bi Bashin Ramadan Zan Iya sittan Shawwal ? - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano
Ku Tura A Social Media


HADISAI INGATATTU SUNZO SUNA KWADAITARWA GAMAI DA AZUMI SHIDA A CIKIN WATAN SHAWWAL, BAYAN KARE AZUMIN RAMADANA,
MANZON ALLAH SAW YACE : DUK WANDA YAYI AZUMIN RAMADANA SANNAN YAYI AZUMI SHIDDA A CIKIN WATAN SHAWWAL KAMAR YAYI AZUMIN SHEKARA NE LADAN SA.
MUSLUM, ABU DAUDA TIRMIZIY NASAIY IBN MAJAH .

AMMA MUN SAN AKWAI WADANDA SHARIA TAYIWA SAUKI SU SHA AZUMI, DAGA BAYA SU RAMA,
KAMAR MACE MAI JININ AL'ADA, DA JININ BIKI,
DA MARA LAFIYA, DA MATAFIYI, DA MAKAMANTANSU.

 YAYA ZA SUYI DA AZUMIN SITTAN SHAWWAL, ALHALIN GA BASHI AKANSU.? AMSA SHINE :
1    A FARA YIN AZUMIN RAMADANA SANNAN AYI SITTAN SHAWWAL. DOMIN WANDA AKE BI BASHI, YA KAMATA YA FARA BIYAN BASHIN, DOMIN KADA YA MUTU DA BASHI AKANSA.
2  YA HALATTA YA FARA DA SITTAN SHAWWAL, MUSAMMAN IDAN BABU LOKACIN DA ZAIYI DUKKAN BIYUN A CIKIN WATAN SHAWWAL DIN.

3  ZAI IYA YIN SITTAN SHAWWAL AJERE KO A RARRABE,
4 BAAYIN NIYYA BIYU AZUMI DAYA KAMAR MUTUM YA HADA A NIYYA DAYA CEWA, DA BASHIN RAMADANA DA SITTAN SHAWWAL A NIYYA DAYA, DOMIN HADISI CEWA YAYI WANDA YAYI AZUMIN RAMADANA SANNAN YA BIYAR DA SITTAN SHAWWAL.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: