Saturday, 15 June 2019
Tsohuwar matar Adam A. Zango 'yar kasar Kamaru Ta Yi Aure

Home Tsohuwar matar Adam A. Zango 'yar kasar Kamaru Ta Yi Aure
Ku Tura A Social Media
Rahotanni sun bayyana cewa tsohuwar matar tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango wadda ya auro daga kasar Kamaru ta sake yin aure inda ta auri wani janar din soja.

Rahoton da Kannywood Exclusive suka wallafa ta bayyana labarin kamar haka:

'Tsohuwar Matar Adam A. Zango, mai suna Ummulkulsum, 'yar asalin kasar Kamaru Mahaifiyar autar diyar sa (Murjanatu) ta yi aure. A jiya Alhamis ne aka daura auren ta da wani Soja mai suna General Ali Bala, a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna a kan sadaki Naira dubu N500. Muna rokon Allah ya basu zaman lafiya.'

Share this


Author: verified_user

0 Comments: