Labarai

Tsaffin gwamonin APC uku Da Ake kyautata zaton Buhari Zai Naɗa ministoci

Akwai kwararan alamu da ke nuna tsohon gwamnan Legas, Akinwunmi Ambode, da takwarorinsa na Adamawa da Bauchi, Mohammed Bindow da Mohammed Abubakar suna cikin wadanda za a nada ministoci a sabuwar gwamnatin Buhari.

Saturday Punch ta ruwaito cewa shugabanin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun yanke shawarar cewa dukkan gwamnonin jam’iyyar da ba su zarce kan mulki ba za su samu kujerar minista a sabuwar tafiyar da za ayi.

Ambode da Bindow da Abubakar ba su yi nasarar zarcewa kan karagar mulki a jihohin su ba.

Ahmed Lawan, sakataren shirye-shirye na jam’iyyar APC ya tabbatar da wannan batun.

Lawan ya ce kawo yanzu shugabanin jam’iyyar ba su nemi jihohi su tura sunan ministoci ba amma ya ce akwai yiwuwar za a nada Bindow minista saboda umurnin da shugabanin jam’iyyar na kasa suka bayar.

Bindow ya sha kaye ne a hannun Ahmadu Fintiri na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) bayan an yi zaben kece raini.

Lawan wanda ke neman kujerar sakataren jam’iyyar na kasa ya ce, “Wannan shine matsayar da shugabanin jam’iyyar suka cimma, babu wanda za a zaba bayan Bindow. Ba su nemi mu aika suna ba. Wannan shine tsarin; duk wata jiha da gwamna bai ci zabe ba, za a nada gwamnan minista.”

Idan aka yi la’akari da wannan matakin, Ambode da ya rasa kujerarsa ga Mista Babajide Sanwo-Olu da Abubakar da ya rasa kujerarsa ga Bala Mohammed suna iya zama ministocin da za a zaba daga jihohin su.

Majiya daga fadar shugaban kasa ta ce Buhari da na kusa da shi suna goyon bayan Ambode saboda haka ana kyautata zaton zai kasance cikin sabbin ministocin.

®Legit.ng

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button


WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?