Tuesday, 25 June 2019
Tirkashi: Fatima Ganduje Ta mayar Da martani Ga Masu zagin mahaifinta

Home Tirkashi: Fatima Ganduje Ta mayar Da martani Ga Masu zagin mahaifinta
Ku Tura A Social Media
'Yar gidan gwamna Ganduje ta maida wa mutanen da suke hawa shafukan sada zumunta suna cin mutuncin mahaifinta martani

- A wannan karon Fatima ta yiwa mutanen zuwan ba zata, inda ta dinga binsu daya bayan daya tana maida musu martani daidai da irin abinda suka rubuta

- Fatima dai ta zama zakaran gwajin dafi, domin kuwa ita ce ta zama jigo wurin kare martabar mahaifinta a shafukan sada zumunta

'Yar gidan gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, wacce ta auri dan gidan gwamnan Ajimobi na jihar Oyo, wato Fatima Ganduje ta fara mayar da martani ga mutanen da suke gaya mata magana marar dadi a shafukanta na yanar gizo.

Fatima wacce ta yi suna wurin rigima da masu sukanta ko sukan mahaifinta akan shafukan sada zumunta, a wannan karon ta yiwa abokanan nata ba zata inda ta hau kan shafinta na Instagram ta mayarwa da wasu mutane da suke aika mata da sako na rashin kirki.

A sakon da ta wallafa na mahaifinta a ranar Uba ta duniya, wani mutumi ya rubuta 'Birin Gwaggo' a kasan rubutun ta, inda ita kuma ta mayar masa da martani da 'Birin Tsula'.


Haka kuma shima wani da yayi magana akan kudin dala da mahaifinta ya ci, Fatima ta mayar masa da martani da cewa 'Shege Banza'.

Wani kuma ya ce mata 'Bakida uba' Fatima ta mai da masa martani da cewa 'Kaima baka da uba shege'.

Sai dai kuma wani daga cikin masu cin mutuncin na ta ya ce "Allah yayi tsinuwa ga mahaifin nata," inda ita kuma ta maida masa zagin nasa da addu'a ta ce: "Kai kuma Allah ya cire maka bakin ciki."

Tun bayan da aka kammala zaben jihar Kano, Fatima ta cire kunya da tsoro a idonta, inda take kare mahaifinta a lokuta da dama idan aka ci masa mutuncin sa a shafukan sada zumunta.
®Legit

Share this


Author: verified_user

0 Comments: