Tuesday, 25 June 2019
Soyayya Da maza masu Aure Ta Fi dadi fiye Da soyayya Da Samari - Budurwa Ta Ba Da dalilai

Home Soyayya Da maza masu Aure Ta Fi dadi fiye Da soyayya Da Samari - Budurwa Ta Ba Da dalilai
Ku Tura A Social Media
- Wata budurwa ta bada wasu dalilai dake nuna cewa soyayya da maza masu aure tafi dadi fiye da soyayya da samari

- Budurwar ta bayyana cewa mace tafi samun kwanciyar hankali da kulawa idan tana soyayya da namiji mai aure

- Inda ta bayyana cewa samarin yanzu dole suje su koyo soyayya a gurin masu aure domin an barsu a baya nesa ba kusa ba

Wani bidiyo yana ta yawo a shafukan sada zumunta, inda yake nuna wata budurwa 'yar Najeriya tana bayyana cewa ta fi son soyayya da maza masu aure da samari.

Budurwar wacce taki bayyana sunanta ta ce ta fadi hakan ne saboda maza masu aure sunfi iya soyayya da kuma kwantar da hankali fiye da samari wadanda basu taba yin aure ba.

A cewar budurwar samari suna bukatar su tsaya su koyi soyayya a wurin masu aure.Ga abinda budurwar ta rubuta:

"Maza masu aure sunfi dadin soyayya fiye da samari, saboda sun iya kalamai masu dadi kuma basu dorawa mace wahala da yawa.

"Idan kina soyayya da namiji mai aure, kin fi samun kwanciyar hankali, kuma suna da kulawa sosai.

"Samari dole suje su koyo soyayya a gurin masu aure, saboda gaskiya babu abinda suka sani akan soyayya.

"Amma idan kina auren mai aure zaki ga salon soyayya kala-kala da kulawa kamar zai cinye ki."

Yanzu dai lamarin soyayya tsakanin samari da 'yan mata ya zama sai du'a'i domin kowa yana soyayyar ne saboda wata bukata ta kanshi ba duka bane ke soyayyar domin Allah.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: