Thursday, 27 June 2019
Shirin fim din Kawaye bai wahalar da ni ba - Aisha Humaira

Home Shirin fim din Kawaye bai wahalar da ni ba - Aisha Humaira
Ku Tura A Social Media


Jaruma fina-finan hausa Aisha Humaira ta bayyana farin ciki ta na kamala shirin fim din Kawaye lafiya tare da bayyana cewa bubu  wani kalubali data fuskanta wajen gudanar da  shirin fim din, kasanewar  shine shirin fim dinta na farko a Duniya.

@ayshatulhumairah ta  bayyana wa OakTV  tace dama can ta saba ganin yadda ake shirya fina-fina hausa shi ya sa gudanar da shirin ba zame mata  wani sabon abu ba kuma bai  zamo mata abun wahala.

Inda  ta kara da cewa kasancewar  shirin fim din wasan kwaikwayone, domin ba gaske  bane wannan dalilin ya bata damar zage dantse wajen ganin ta taka rawar gani yadda ya kamata  ta a shirin fim, inda ta bayyanan jin dadin aikin da abokan aikin bisa hadin kai data samo dari bisa dari a tare dasu.

A karshe tayi yiwa kannywood fatan cigaba tare da fatan ganin kannywood ta bukasa fiye da yadda take.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: