Saturday, 29 June 2019
Shin Da Gaske Ne Jarumi Shuaibu Lawal, Kumurci Ya Mutu ?

Home Shin Da Gaske Ne Jarumi Shuaibu Lawal, Kumurci Ya Mutu ?
Ku Tura A Social Media
Rahotannin bogi a Shafin Fesbuk, sun tura babban Jarumin masanaantar shirya Fina-finan Hausa na Kannywood Lahira kuma labarin bogin yayi yawo sosai.

Wannan kuwa ba kowa bane illa Jarumi Shuaibu Lawal Kumurci.

To sai dai Jarumin a wani sabon faifayin Bidiyon daya fitar da yammacin yau Asabar, Shuaibu Lawal Kumurci, ya karyata batun da cewar karya ake yi bai mutu ba yana nan a raye.

Shuaibu Lawal Kumurci, ya ce masu yi mishi fatan mutuwa su kara hakuri lokaci ne bai yi ba amma idan lokaci yayi babu shakka zai mutu.

Shafin Hausaloaded ta samu karin haske daga shafin Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewar jarumin ya kara da cewa ita Mutuwa lokaci ne ko dai su suga tashi mutuwar ko kuma shi yaga tasu, a cikin bayanin sa ma sai daya jawo Ayar alkur'ani mai bayanin mutuwa.

Zuwa yanzu Jaridar Dimokuradiyya tare da hadin gwiwar wasu manyan Jaridun ciki da wajen Najeriya sun hada gidauniyar yaki da labaran Bogi da kuma satar fasaha.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: