Friday, 7 June 2019
Sharhin Fim Din Larai Ko Jummai

Home Sharhin Fim Din Larai Ko Jummai
Ku Tura A Social Media
Suna: Larai Ko Jummai
Tsara Labari: Nazir Alkanawi
Kamfani: Abnur Entertainment
Shiryawa: Abdul Amart
Umarni: Sadik N. Mafiya
Jarumai: Garzali Miko, Adul M. Sharif, Bashir Nayaya, Ladidi Fagge, Maryam Yahya, Amal Umar, Asma’u Sani da sauransu
Sharhi: Hamza Gambo Umar
A farkon fim din an nuna Zuwaira (Ladidi Fagge) ta tsaya a kofar dakin kishiyar ta tana sababi saboda tayi mugun mafarki wanda take zargin kishiyar ta ce take yi mata asiri, a sannan ne kishiyar ta ta Azumi (Asma’u Sani) ta fito tana tambayar ba’asi wanda hakan yasa suka soma kokarin yin rigima amma Azumi bata biyewa Zuwaira ba har zuwa lokacin da mijin su (Bashir Na Yaya) ya fito daga dakin Azumi ya soma bawa Zuwaira rashin gaskiya saboda sanin cewa a ko yaushe itace ke neman rigima da kishiyar ta Azumi. A wannan lokacin ne kuma ‘ya’yan su dake kwance a daki wato Larai (Maryam Yahya) da Jummai (Amal Umar) suka fito daga cikin daki suka soma rarrashin iyayen su akan su daina rigima. Haka zaman gidan ya cigaba Zuwaira bata son a zauna lafiya haka kuma ba ta so ‘yar ta Jummai tayi kyakykyawar mu’amula da kishiyar ta Azumi ko kuma ‘yar kishiyar ta Larai.
Wata rana Umar (Garzali Miko) ya dawo daga birni inda yake aikin gyaran mota a can, bayan dawowar sa ne suka hadu da abokin sa Umar (Abdul M. Sharif) wanda sukayi matukar shakuwa da juna, a lokacin da suka fara ganin Larai da Jummai sai Umar ya nuna yana son auren Larai yayin da ita kuma Jummai taji tana son Umar din saboda ganin ya zama dan birni ita kuma macece me son mutumin birni, sai dai kuma tuni Nura shima ya gan ta yaji yana son ta wanda hakan ne yasa Umar ya bayyana soyayyar shi ga Larai yayin da Nura ya nuna yana son Jummai, duk da kasancewar Jummai din ba shi take so ba amma ganin Umar ya nuna yana son ‘yar uwarta sai ta danne son da take yi masa ta karbi soyayyar Nura duk suka soma nuna wa juna soyayya wanda har daga baya Umar da Nura suka sanar da magabatan su don a nema musu auren ‘yan matan, bayan Mahaifiyar Umar taje gidan su Larai ta sanar da maganar neman auren su Nura ga iyayen su Larai, a sannan ne mahaifiyar Jummai wato Zuwaira ta nuna tana son ganin su Nura don bata san su a ido ba kuma tana fatan ba za’a yiwa ‘yar ta kishiya ba, haka bayan shigar su daki da ‘yar ta Jummai ta kara nuna bata yarda a aure ta ayi mata kishiya ba amma sai Jummai ta nuna kishiya indai irin mahaifiyar Larai ce wato Zuwaira ba laifi bane don an yi mata, anan ne Zuwaira ta nuna rashin jin dadin ta kan abinda Jummai ta fada. Ana tsaka da haka kuma sai Nura da Umar suka zo gaisar da iyayen su Larai, anan ne Zuwaira ta tambayi wanda yake son ‘yar ta Jummai sai aka nuna mata Nura wanda ke sanya da kaya na marasa wadata, hakan yasa ta kalli Umar ta gan shi sanye da kaya masu tsada kuma ta ga da zasu tafi shi Umar din ya dauki kyautar kudi ya bawa mahaifin su Larai din. Hakan ne ya tashi hankalin Zuwaira ta jawo ‘yar ta daki tana nuna mata illar auren talaka irin Nura, a sannan ne ‘yar ta Jummai ta nuna a baya Umar ta so dole ce tasa ta rabu dashi, jin hakan ne kuma ya karawa Zuwaira kwarin guiwa taje ta shirtawa Mahaifin su Larai makirci har ya amince aka canja tsarin lamarin, cikin lokaci kadan aka sanar da nura baza’a ba shi auren Jummai ba Umar ne zai aure ta shi kuma Nura din ya auri Larai, gaba daya Nura da abokin sa Umar ba su ji dadin hakan ba amma ganin manya sun saka baki akan maganar sai suka hakura suka amince da bukatar iyayen su wanda cikin lokaci kadan aka daura auren Nura da Larai a madadin shi da Jummai, haka itama Jummai aka daura auren ta da Umar a madadin ita da Nura.
Sai dai kuma bayan auren ne Umar yaja Nura suka koma birni don yin sana’a amma sai Nura yayi arziki cikin dan lokaci kadan ya zamo yana samun kudi fiye da Umar, dawowar sa birni kuma sai ya sayawa iyayen su Larai kayan abinci masu yawa wanda shi kuma Umar dawowar sa bai kawo komai ba. Hakan ne ya tashi hankalin Zuwaira ta je ta dauko ‘yar ta Jummai daga gidan miji ta dawo da ita gida saboda mijin Jumman bashi da wadata kamar ta abokin sa Nura. Sai dai kuma Jummai tsakar dare ta gudu ta koma dakin mijin ta, yayin da washe gari Zuwaira ta tsorata saboda zaton ko yawon duniya Jummai ta tafi, amma daga baya da ta gane cewar gidan mijin ta ta koma sai ta saduda ta tuba aka zauna lafiya.

Abubuwan Birgewa:

1- An yi kokari wajen samar da wuraren da suka dace da labarin wato (location)
2- Fim din ya fadakar, kuma labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isar wa.
3- Camera ta fita radau, kuma an yi amfani da salon daukar hoton da ya dace.

Kurakurai :

1- An nuna Nura (Abdul M. Sharif) da abokin sa Umar (Garzali Miko) sun soma soyayya da su Larai a lokaci daya, sannan kuma sun yi aure a rana daya, haka kuma matayen su su Jummai sun fara nakuda a lokaci daya sun haihu a lokaci daya. Ya dace a bambanta lokacin haihuwar ta matayen su ko da ta hanyar nuna tazarar kwana daya ne a tsakani, idan kuma a ranar ake son su haihu to ya dace a nuna cewar daya ta haihu da safe daya kuma da yamma, hakan ne zai sa me kallo ya gamsu da cewar zahirin abinda zai iya faruwa yake kallo ba fim ko tatsuniya ba.
2- Shin Umar (Garzali Miko) ba shi da mahaifi ne? Har fim din ya kare me kallo bai ga mahaifin Umar ba kuma ko a baki ba’a ambace sa ba. Idan kuma ya rasu ne to ya dace ko a baki ne a fada.
3- Lokacin da Nura da Umar suka shiga gidan mahaifiyar Umar (Garzali Miko) da nufin su sanar mata da kudurin su na son aje a nemo musu auren Larai da Jummai, me kallo yaga Umar yabar keken sa a kofar gida sun nufi cikin gidan kai tsaye, amma bayan shigar su sai aka ga Umar rike da keken a hannun sa yana turawa, shin komawa yayi ya dauko keken?

4- Me kallo yaga mahaifiyar Umar (Garzali Miko) taje nemawa Umar da Nura auren su Jummai, tun da an nuna mahaifin Nura a fim din to ya dace ace shi yaje nemawa dan sa aure ba mahaifiyar abokin dan sa ba, haka kuma shima Umar din ya dace ace idan ma bashi da mahaifi to ko kawunsa ne ya dace ace shi yazo nema masa aure ba mahaifiyar sa ba saboda a bisa al’ada zuwan kawun sa sai yafi muhimmanci da kwarjini fiye da zuwan mahaifiyar sa.

5- Lokacin da Mahaifiyar nura ta gama bayani akan nemawa ‘dan ta da abokin sa auren su Jummai, mahaifin su Jummai din ya bukaci su yi addu’a kafin su tashi yayin da ya ambaci wasu surori don a karanta amma sai akaji duk sun maimaita surorin kamar yadda ya fada ba tare da karantawa ba, shin gaba dayan su matan ba su da ilimin addini ne? Idan kuma ba su fahimci yanayin yadda za su karanta surorin bane to ya dace mahaifin su Jummai yayi musu karin bayani tun da an nuna cewar malami ne a cikin garin.

Karkarewa:

Labarin ya tafi kai tsaye har ya dire bai karye ba, haka kuma fim din ya fadakar domin an nuna cewar duk abinda yake rabon ka za ka sameshi ko a kusa ko a nesa, sai dai kuma akwai abubuwan da ya kamata a kara inganta su. Wallahu a’alamu!

Share this


Author: verified_user

0 Comments: