Thursday, 6 June 2019
Rikicin Masarautar Kano: Sarkin Kano Ya Mayar Da Martani A Kan Tuhumar Da Ganduje Yake Masa

Home Rikicin Masarautar Kano: Sarkin Kano Ya Mayar Da Martani A Kan Tuhumar Da Ganduje Yake Masa
Ku Tura A Social Media


Daga Wakilinmu Yaseer Kallah

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya mayar da martani a kan takardar tuhumar da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tura masa.

The Nation ta yi rahoton cewa Sarkin, wanda ya shaida karbar takardar tuhumar daga gwamnati, ya bayyana cewa yana kan nazarin abin da tuhumar ta kunsa.

Gwamnatin Ganduje ta tuhumi Sarkin a kan zargin almubazzarancin naira biliyan biliyan 3.4, mallakin masarautar. Ta kuma bai wa Sarkin awanni 24 a kan ya kare kanshi daga zargin.

Da yake mayar da martani ta bakin shugaban ma'aikatansa, Munir Sanusi, Sarkin ya ce majalisar masarautar na nazarin abin da tuhumar ta kunsa.

"Mun amshi takardar tuhumar a yau (Alhamis). Gwamnatin jihar ta nemi Mai Martaba Sarki da ya bayar da amsar tuhumar a cikin awanni 24. Majalisar masarautar tana nazarin abin da tuhumar ta kunsa."

Share this


Author: verified_user

1 comment: