Friday, 28 June 2019
Next Level or Next Cable ? Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Mai Girma Shugaban Kasar Nigeria - Ty Shaba

Home Next Level or Next Cable ? Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Mai Girma Shugaban Kasar Nigeria - Ty Shaba
Ku Tura A Social MediaA yau shafin Hausaloaded blog munzo muku da wani labari da jarumi Ty shaba ya walafa a shafinsa na Instagram ga jawabinsa.

"Next level or Next cable? BUDADDIYAR WASIKA: Zuwa ga Mai girma shugaban kasar Nigeria  @MBuhari Muhammadu Buhari. @muhammadubuhari 
Anyi zabe lafia, Allah ya baka nassara a karo na biyu, muna tayaka murna kwarai da gaske duba da irin jajircewar da abokan sana’ata Yan FIM kannywood sukayi wurin tallata manufar ka.  Hakika sunyi kokari wurin yada manufarka duk da cewa gwamnatinka bata tsinana masu ko nace mana komai ba a cikin hanyar sana’ar FIM a zahiri. Ba ina nufin samun kudin da daidaikun masu shirya fina finai sukayi a iya bakin aljihunsu ba,  amma ina nufin a masana’antar film baki Daya.

Mai girma shugaban kasar Nigeria Yan FIM suna bukatar agaji wurin inganta sana’arsu da samun sanin makamar aiki ta yadda zasu samu kwarewa ta hanyar samar da fina finai na ilimin dabbaka al’ada, Zamantakewa, kaucewa ayyukan ta’adda da shaye shayen miyagun kwayoyi da suka addabi al’umarmu kamar yadda gwamnatin baya tayi wurin zuba kudi fiye da NAIRA biliyan uku (3) a harkokin fina finai wanda dayawa Yan FIM sunci moriyar “project act” 
Gwmnatin baya takai masu sana’ar shirya fina finai kasashen waje domin karo ilimin sanin sana’ar wanda dayawa daga kannywood sunci moriyar shirin na gwamnatin baya. Haka zalika  gwamnatin baya fiye da NAIRA miliyan 1000 Daya aka bayar domin zuwa birnin Los Angeles na kasar amurka da sauran kasashen duniya domin daukar horo akan magance yakin boko haram a arewa maso gabas a Nigeria.

Ya mai girma shugaban kasa samar mana da wani kebebben wuri kamar CULTURE FILM VILLAGE a karkashin kulawar malamai, masu ruwa da tsaki a harkokin fina finai da kwararrun malaman jami’a masana harkokin fina finai a ilimance zai bada dama wurin kaucewa ayyukan ashsha da al’umma a kullum suke korafi akai. Mr PRESIDENT a kula damu da sauran al’umar Nigeria wurin ingatta rayuwarmu baki daya. Allah ya shige maka  gaba yayi riko da mulkinka.

CONGRATULATIONS your excellency.

TY Shaban (shaba)
Film practitioner kannywood"

Share this


Author: verified_user

0 Comments: