Sunday, 23 June 2019
Next Level: An bayyana lokacin da Buhari zai nada sabbin ministoci

Home Next Level: An bayyana lokacin da Buhari zai nada sabbin ministoci
Ku Tura A Social Media
Akwai alamun cewa Shugaban Kasa Muhmmadu Buhari zai aikewa Majalisar Dattawa sunayen ministocinsu domin tantancesu a watan Yuli inji wani bincike da Sunday Punch ta gudanar.

Wani tsohon ministan da ya yi aiki a zangon mulkin Buhari na farko ya ce ya yi imanin cewa Buhari zai aike da jerin sunayen ministocinsa da wuri domin kaucewa maimaita irin jinkirin da aka samu a zangon mulkinsa na farko inda ya yi watanni shida kafin ya fitar da sunayen ministocin.

Bugu da kari, ministan ya ce shugaban kasar ya san tsare-tsaren majalisar cewa za su dawo daga hutu a ranar 2 ga watan Yuli.

Ana sa ran sanatocin za su tafi hutun watanni buyu daga ranar 26 ga watan Yuni.


Majiyar ya kuma ce tsaffin ministocin ba su da tabbas din cewa shugaban kasar zai sake zabensu a zangon mulkinsa na biyu.

Ya ce, "Mun ji kishin-kishin cewa akwai yiwuwar shugaban kasa zai mika wa majalisar dattawa sunayen ministocinsa a wata mai zuwa.

"Ina tunanin ya san cewa sanatocin za su sake tafiya hutu kafin karshen watan Yuli. Saboda haka zai yi kokarin tura wa majalisa sunayen ministocinsa da zarar sun dawo a ranar 2 ga watan Yuli.

"Duk da cewa jam'iyyar mu ta APC ne ke jan ragamar majalisar, Bana tunanin zai dace a kira sanatocin su zo tantance ministoci bayan sun tafi hutu."

Da aka masa tambaya ko an bukaci ya mika takardun sa domin yiwuwar sake zabensa a matsayin ministoci a zango na biyu, ya ce a'a,  "shugaban kasa ne kawai ya san wadanda za su dawo".

Share this


Author: verified_user

0 Comments: