Friday, 28 June 2019
Na fiso na fito a matsayin fitsararriya a film -Maryam Yahaya

Home Na fiso na fito a matsayin fitsararriya a film -Maryam Yahaya
Ku Tura A Social Media

Fitacciyar jarumar wasan hausarnan Maryam Yahaya ta bayyana cewa fison ta taka rawa a film a matsayin fitsararriya, Maryam Yahaya ta bayyana hakanne acikin tattaunawarta da shirin Taurarunmu na tashar Freedom Radio a daren jiya Alhamis, sai dai tace a zahiri ita ba fitsararriyar bace, tana son hakanne saboda yadda ta fahimci masoyanta suna son ganin ta taka irin wannan rawar.

A hirar ta jiya dai jarumar ta tattauna batutuwa da dama musamman irin rawar da ta taka a film din SARINA, ta kuma yi fatan alkhairi ga daukacin masoyanta.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: